Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

1984: Yadda Aka Dakile Satar Umaru Dikko

A shekarar 1984 wata kungiya ta 'yan Najeriya da Isra'ilawa ta yi yunkurin sacewa da mayar da tsohon Ministan Najeriya U...


A shekarar 1984 wata kungiya ta 'yan Najeriya da Isra'ilawa ta yi yunkurin sacewa da mayar da tsohon Ministan Najeriya Umaru Dikko zuwa gida daga London. An zargi Alhaji Umaru Dikko ne, wanda ya tsere daga Najeriya bayan wani juyin mulkin soja, da sace dala biliyan daya daga aljihun gwamnatin Najeriya.

Wani matashin jami'in kwastam na Burtaniya, Charles David Morrow, shi ne ya yiwa shirin sace tsohon ministan kafar ungulu; yanzu kuma ya bayyanawa shirin Witness na Sashen Watsa Labarai ga Kasashen Waje na BBC bayanin yadda abin ya faru.

Wata rana Umaru Dikko ya fito daga gidansa da ke unguwar masu hannu-da-shuni ta Bayswater da ke London; kafin kiftawa da bismillah wasu mutane su biyu suka cukume shi suka tura shi cikin motarsu.

Shekara guda bayan nan, Umaru Dikko ya shaidawa BBC cewa, "Ina tuna yadda aka cakume ni aka kuma cusa ni cikin wata motar safa karfi da yaji, sannan wani bawan Allah ya zauna a kaina; da kuma yadda aka sanya min sasari a hannu da kafa".

Alhaji Umaru Dikko ne ministan sufuri a gwamnatin Shehu Shagari har zuwa lokacin da sojoji suka kifar da ita a karshen shekarar 1983. Ya tsere zuwa London ne saboda zarginsa da sababbin shugabannin Najeriya suka yi da almubazzaranci--zargin da ya sha musantawa.

Bayan an lakaba masa taken "Mutumin da aka fi nema a Najeriya" an shirya wani shiri na yadda za a dawo da shi gida tare da kudi.

Shirin ya kunshi sace Umaru Dikko da dura masa kwayoyi da kuma kunsa shi a cikin wani akwaku sannan a sanya shi a jirgi a mayar da shi Najeriya--a raye.

Likita dan Isra'ila. 

Wani wanda ake zargin tsohon ma'aikacin hukumar leken asiri ta Isra'ila ne, Alexander Barak, aka dauka ya jagoranci shirin. A cikin 'yan tawagarsa kuma akwai wani jami'in leken asiri na Najeriya, Manjo Mohammed Yusuf, da wasu 'yan kasar Isra'ila Felix Abitbol da Dokta Lev-Arie Shapiro, wanda aka dorawa alhakin yiwa Dikko allurar barci.

Masu satar sun sauya mota a wani wurin ajiyar motoci da ke kusa da gidan ajiyar namun daji na London sannan suka dauki hanyar filin jirgin sama na Stansted, inda wani jirgin saman Nigerian Airways ke jira. A nan suka yiwa Dikko allurar barci, sannan suka saka shi a cikin akwakun.

Shi ma likitan dan Isra'ila ya shige cikin akwakun da magunguna don tabbatar da cewa Dikko bai mutu a hanya ba; Barak da Abitbol kuma suka shiga wani akwakun na daban, sannan aka like su duk.

A gefen da jiragen daukar kaya ke sauka a filin jirgi na Stansted mai tazarar kilomita sittin da shida daga birnin London kuwa, wani jami'in diflomasiyyar Najeriya ya kagu a kawo akwakun. A daidai lokacin shi ma matashin jami'in kwastam Charles David Morrow yana bakin aiki.

Jakar diflomasiyya

A cewar Morrow, "Har zuwa misalin karfe uku na yamma ranar kamar ko wacce rana ce; a lokacin wasu jami'ai suka zo suka ce akwai kayan da za a dora a jirgin Nigerian Airways 707, amma mutanen da suka kawo kayan ba sa so a shigar da su cikin littafi.

"Sai na gangara kasa don in ga ko su wanene kuma me ke faruwa. A nan na samu wani jami'in diflomasiyyar Najeriya mai suna Mista Edet. Ya nuna min fasfo dinsa ya ce kayan na diflomasiyya ne. Kasancewar ni ba sanin harkar diflomasiyya na yi ba, sai na tambaye shi menene a ciki. Ya shaida min cewa takardu ne kawai da wasu abubuwa".

Babu wanda ke aiki a Stasted a lokacin da ya taba yin kacibis da jakar diflomasiyya, don haka Mista Morrow ya je ya bincike yadda ake yi da su.

A daidai lokacin wani abokin aikinsa ya dawo daga gefen daukar fasinjoji da wani labari mai ban mamaki: wata sanarwa da hedkwatar 'yan sanda ta Scotland Yard ta fitar tana bayyana cewa an sace wani dan Najeriya kuma ana zargin za a yi fasa-kwaurinsa zuwa wajen Burtaniya.

Sakataren Umaru Dikko ne ya tuntubi 'yan sandan bayan ya shaida sace shi ta tagar gidansa.

Da jin wannan labari sai Mista Morrow ya tsinci kansa yana fuskantar gagarumar matsala.

A cewarsa, "Nan take na yi lissafi. A bisa karantarwa kwastam, na leka ta taga na dubi wadannan akwaku guda biyu na ga girmansu ya kai yadda za a iya cusa mutum a cikinsu. Sannan kuma ga jirgin Nigerian Airways 707 wanda ba kasafai mu kan gan shi ba. Ba sa so a shigar da bayanan akwakun a cikin littafi saboda ba sa so a san sun wuce. Sannan kuma kayan da za a saka a jirgin ba su da yawa.

"idan kana so ka boye bishiya, to ka boye ta a cikin daji, kada ka fito da ita sarari a tsakiyar Essex".

Dan ka'ida

Sai dai kuma Yarjejeniyar Vienna ta haramtawa jami'an kwastam bude jakunkunan diflomasiyya. Don haka Mista Morrow ya dauki waya ya kira Ma'aikatar harkokin Waje ta Burtaniya.

"Kafin jaka ta zama 'jakar diflomasiyya' wajibi ne a rubuta mata kalmar 'jakar Diflomasiyya' karara sannan kuma a hado ta da jami'in da ya dace dauke da takardun da suka dace. Ba tantama suna tare da jami'in diflomasiyyar Najeriya--ya ma nuna min fasfonsa--amma ba su da cikakkun takardu kuma ba a rubuta 'Jakar Diflomasiyya' ba', inji Mista Morrow.

Saboda haka aka yanke shawarar cewa za a iya bude akwakun--amma dole a bi ka'ida. Hakan kuma na bukatar kasancewar wani jami'in diflomasiyyar Najeriya, kuma ga shi a kusa. A halin da ake ciki dai tuni har an dora akwakun a kan wasu kekunan daukar kaya na musamman, jira kawai suke yi a dura su cikin jirgi.

"Jami'in dake kula da kaya, Peter, ya doki murfin akwaku, ya daga shi; nan take sai jami'in diflomasiyyar na Najeriya, wanda ke tsaye a gefe na ya fita a guje kamar an razana bera", inji Mista Morrow.

"Kar a manta muna filin jirgi ne wanda sarari ne ba komai. Da ya yi gudun mita hudu da rabi sai ya tsaya da ya fahimci ba mai binsa.

"Peter ya leka akwakun ya ce 'akwai mutane a ciki!'"

Nan da nan Mista Morrow ya dauki waya ya kira lamba 999.

Mista Morrow ya tuna abin da ya fada: "Suna na Morrow, jami'in kwastam a Stansted. Mun samu mutane a cikin akwaku. Kuna ganin za ku iya turo wani ya gani?

"Sai suka ce: 'A mace ko a Raye?'

"Sai na ce: 'Ni ma ban sani ba'.

"A nan ne suka ce: 'Za mu turo motar daukar marasa lafiya'".

Bayan rabin sa'a 'yan sanda suka fara hallara, suka kuma bude akwaku na biyu. A ciki suka samu Umaru Dikko bai san inda yake ba, da kuma likitan Isra'ila ya yi zuru-zuru.

"Ba riga a jikin Dikko; an saka mishi wata na'ura mai auna bugun zuciya da wani bututu a makogwaronsa saboda kar hanyar numfashinsa ta toshe. Ba takalma ko safa a kafarsa sai sasari", inji Mista Morrow.

Masu satar ba su yi nadama ba sam. A cewarsu babu bata-garin da ya kai Umaru Dikko a duk fadin duniya.

Daga bisani aka yankewa jami'in leken asirin na Najeriya da Isra'ilawa uku hukuncin zaman kaso a Burtaniya.

Hakazalika dangantakar tsakanin Burtaniya da Najeriya ta durkushe, ba a mayar da ita ba sai bayan shekaru biyu. Su kuwa gwamnatocin Najeriya da Isra'ila sun yi ta shan laya cewa ba su da hannu a satar ta Umaru Dikko.

Sai bayan shekaru goma Umaru Dikko ya koma Najeriya; har yanzu kuma yana zaune a can.

Shi kuwa Mista Morrow ya samu yabo daga shugaban hukumar kwastam ta Burtaniya, wanda ya bayyana al'amarin da cewa "abu ne mai rikitarwa", saboda matakan da ya dauka.

-BBC HAUSA

No comments