Sarakunan gargajiya a Jamhuriyar Nijar sun bukaci gwamnati ta kafa dokar da ke hana aurar da ‘yan mata matukar dai shekarunsa ba...
Sarakunan gargajiya a Jamhuriyar Nijar sun bukaci gwamnati ta kafa dokar da ke hana aurar da ‘yan mata matukar dai shekarunsa ba su kai 18 ba a duniya. Wannan dai na kunshe a cikin sanarwar bayan taron da Sarakunan suka gudanar tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya kan yadda za a rage haihuwa a kasar kamar yadda gidan Rediyon Faransa ta labarto.
Babbar manufar shirya wannan taro ita ce tattara ra’ayoyi daga
sarakunan gargajiya da kuma shugabannin addinai kan yadda za a tunkari matsalar
karuwar jama’a a jamhuriyar Nijar, kasar da alkaluma suka bayyana cewa a can ne
mata suka fi yawan haihuwa a duk fadin duniya.
A sanarwar da suka fitar karshen wannan taro na yini, sarakunan sun
bukaci gwamnatin jamhuriyar Nijar ta kafa dokar da ke haramta aurar da ‘yan
mata matukar dai shekarunsu ba su kai 18 ba a duniya, tare da kara bai wa
sarakunan makudaden kudade a cikin kasafin kasar na kowace shekara.
Illahiran sarakunan sun sun dauki alkawarin cewa daga yanzu ba za
su sake halartar bikin daurin auren yarinyar da ba ta cika shekaru 18 ba a
duniya, sannan suka dauki alkawarin ci gaba da wayar da kawunan al’umma dangane
da muhimmancin sanya yara makaranta da kuma hana auren gaggawa.
A jawabinsa wajen rufe wannan taro, ministan lafiya da kuma
kyautata rayuwar al’umma, Dr Iliassou Idi Mainassara, ya ce zai iya kokarinsa
domin gabatar da shawarwarin sarakunan gaban gwamnatin kasar.
No comments