Ministan Kimiyya da fasaha, Dr. Ogbonnaya Onu ya bayyana cewa, Nijeriya na kan hanyar ci gaba game da matsalolin tsaron da suka ...
Ministan Kimiyya da fasaha, Dr. Ogbonnaya Onu ya bayyana cewa, Nijeriya na kan hanyar ci gaba game da matsalolin tsaron da suka mata katutu, inda ya ce a maimakon zuwa kasashen waje da ake yi ana sayo makamai, akwai bukatar kasar ta bude kamfaninnika da za su rika kera makamai domin magance matsalar tsaron kasarnan.
Ya bayyana cewa, dalilin matsalolin tsaron, Nijeriya za ta tashi tsaye wajan samarwa kanta mafita.
Yayi kiran cewa, maimakon zuwa kasashen waje ana siyo makamai, abin da ya kamata a yi a Nijeriya shi ne a samar da kamfanonin da za su rika kera makaman a cikin gida.
No comments