Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Abin Da Cristiano Ronaldo Ya Ce Kan Hamayyarsa Da Leo Messi

Cristiano Ronaldo ya karyata ikirarin cewa burinsa ya sha gaban Messi a yawan samun nasarori musamman kyautar gwarzon É—an wasan ...



Cristiano Ronaldo ya karyata ikirarin cewa burinsa ya sha gaban Messi a yawan samun nasarori musamman kyautar gwarzon É—an wasan duniya.

Ronaldo na mayar da martani ne ga Editan mujallar Kwallo ta France Football Pascal Ferre wanda ya ce burin Ronaldo shi ne ya zarta Messi.

ÆŠan wasan na Manchester United ya ce “Ferre ya Æ™irÆ™iri labarin ne kan wata manufarsa kan kyautar gwarzon É—an wasan duniya da ba a bayar ba a 2020 saboda annobar korona.”

A sakon da ya wallafa a shafukansa na Facebook da Instagram kafin sanar da Messi a matsayin wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or a ranar Litinin ya ce “Pascal Ferré ya yi Æ™arya ne ta hanyar amfani da sunana domin tallar kansa da kuma tallar jaridar da yake yi wa aiki.

A cikin saƙon, Ronaldo ya ce yana taya duk wanda ya lashe kyautar murna.

Messi, wanda ke taka leda yanzu a Paris St-Germain, a ranar Litinin ya lashe kyautar Ballon d'Or karo na bakwai, a yayin da Ronaldo wanda ya karbi kyautar sau biyar ya ƙare a matsayi na shida a duniya a bana.

No comments