Adadin Wadanda Korona Ta Kashe A Duniya Ya Zarta Mutum Miliyan Biyar

 


BBC ta labarto cewa; masu bincike a Amurka sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon annobar korona a duniya sun zarta miliyan biyar.

Alkaluman da jami’ar Johns Hopkins ta wallafa a shafinta ya tattaro bayanai daga sassan duniya na adadin mutanen da suka kamu, da ma wadanda suka mutu sanadin kamuwa da cutar.

A cewar rahoton Amurka ke kan gaba da yawan mutanen da annobar ta kashe da kusan mutum 750,000.

Sai Brazili mai mutum 600,000, sai kuma Indiya da ke ta uku da 450,000.

Post a Comment

0 Comments