Daga Fatima Idris Zaria A ci gaba da binciken da ake gudanarwa akan kalubale da nasarori da ake samu a bangaren ilmi a kasa baki...
Daga Fatima Idris Zaria
A ci gaba da binciken da ake gudanarwa akan kalubale da nasarori da ake samu a bangaren ilmi a kasa baki daya, jaridarmu ta ziyarci Kwalejin ilmi dake Zariya a jihar Kaduna wanda a halin yanzu Dakta Suleiman Balarabe ne shugabancin riko.
Abu na farko da ake fara lura da shi a irin wadannan cibiyoyi shi ne alakar shugaba da wanda yake yi wa shugabanci.
Hakan yasa jaridarmu ta nemi jin ta bakin daya daga cikin ma'aikatan da suke cikin wannan Kwalejin domin jin wani halin suke ciki game da walwala da jin dadi na ma'aikata baki daya?
Malam Jamilu Bello Dogarawa ya yi godiya da ziyarar kuma ya ji dadin tambayar da a kai masa game da shugabancin Dakta Suleiman Balarabe a FCE Zaria a halin yanzu.
Dogarawa ya ce, a gaskiya daga lokacin da aka ayyana Dakta Suleiman a matsayin shugaban riko take Malamai da dalibai da mu kanmu ma'aikata muka fara murna tare da fatan Allah ya tabbatar da shi a matsayin shugaba na dindindin domin za a sami canji a bangarori da dama.
Dogarawa ya ce, daga hawansa shugaban riko a halin yanzu komai ya canza a bangarori daban-daban ciki harda walwala da jin dadi na ma'aikata da dalibai a makarantar baki daya.
Tabbas da yawan mutanen da suka bayyana ra'ayinsu game da hanyoyin bunkasa ilmi a FCE Zaria sun yi kyakkyawar shaida ga kamun ludayin shugaban riko na yanzu Dakta Suleiman Balarabe.
Mun bincika yadda muhallin kwana da ajujuwa suke domin shaida kalamun alkairi da ake yi wa shugaban rikon wanda tabbas lamarin na bukatar jinjinar ga shugaban riko wato Dakta Suleiman Balarabe.
Matsalar wutar lantarki da ruwan sha da dalibai ke fama da shi a wasu makarantu wanda hakan na yi wa karatunsu tsaiko, to a FCE Zaria an dakile wannan matsalar a halin yanzu domin lamarin wuta lantarki da ruwan sha da maganar tsaro shugaban na yin bakin kokarinsa bisa bincike da aka gudanar.
Haka zalika bincike ya shaida kawowa dalibai manyan motocin zirga-zirga domin rage musu wahalar biyan kudin mota mai yawa ta inda suke biyan kudi kadan domin kawo su makarantar daga Anguwarsu kuma a koma da su anguwanninsu ga wanda suke da nisa tsakaninsu da harabar kwalejin.
Akan sami tsaiko a bangaren biyan albashi a wasu cibiyoyin dake kai har a tsunduma yajin aiki to bisa haka ne Malam Dogarawa ya ce, su a FCE Zariya karkashin shugaban riko wato Dakta Suleiman Balarabe babu wata matsala sai ma godiya da za su yi ma shugaban rikon.
A duk cibiyoyin ilimi akan sami kungiyoyi kamar kungiyar malamai da kungiyar ma'aikata da kungiyar dalibai kuma suna taka rawa a ci gaban ilmi da sauran fannoni in dai akwai fahimtar juna tsakaninsu da hukumar makaranta to a FCE Zaria ya lamarin yake ne?
Malam Dogarawa ya tabbatar da kyakkyawar fahimta tsakaninsu da shugaban riko na FCE Zaria Dakta Suleiman Balarabe, ya kara da cewa, dukkannin kungiyoyin gami da masarautar Zazzau duk babu wanda bai fatan Dakta Suleiman Balarabe ya sami mukamin dindindin don ganin kokarin da yake a bangaren ilmi Zariya da kasa baki daya.
Karshe Malam Jamilu Bello Dogarawa ya yi kira ga dukkan shugabannin kungiyoyin dake FCE Zaria da su hada kai don ganin aikin da shugaban rikon ke yi ya ci gaba.
Kuma ya yi kira ga hukumar ilmi na kasa baki daya da su tabbatar masu da Dakta Suleiman Balarabe a matsayin shugaba na dindindin don kokarinsa da hazakarsa a bangaren bunkasa ilmi a wannan kwaleji.
Ya yi fatan Dakta Suleiman Balarabe zai kara kaimi akan taimakon da yake yi don ci gaban ilmi a wannan makaranta mai albarka ta FCE Zariya.
Ya zuwa kawo wannan rahoto kungiyoyi masu zaman kansu na ta tururuwar kawo karamci ga shugaban bisa irin taimako da yake yi a bangaren ilmi a Zariya da jihar Kaduna baki daya.
No comments