Ɗaruruwan mutane ne a garin Chiromawa da ke waje-wajen birnin Kano su ka ƙwaci wani shugabansu, Alhaji Yusuf Nadabo, mai shekara...
Ɗaruruwan mutane ne a garin Chiromawa da ke waje-wajen birnin Kano su ka ƙwaci wani shugabansu, Alhaji Yusuf Nadabo, mai shekara 80.
Shi dai Nadabo shine mai gidan man Chiromawa Petroleum Station, sannan shine Sarkin Noman Kano.
DAILY NIGERIAN HAUSA ta samu bayanan cewa su dai ƴan ta'addan, waɗanda su ka zo da muggan makamai domin yin garkuwa da Nadabo, sun dira a ofishin sa ne da ke Bakin Tasha da misalin ƙarfe 7:35, in da su ka riƙa harbi sama domin su razana jama'a.
Ai kuwa harbin nan na su bai razana al'umma ba, inda su ka tunkari ƴan ta'addan, har ma wani a cikin jama'ar garin ya samu raunuka na harsashi, kamar yadda wata majiya ta shaidawa wannan jarida.
"Ƴan ta'addan ba su samu nasara ba sabo da sun zo ne a ranar kasuwa. Akwai jama'a da dama ana ta hada-hada a yankin," in ji shaidun gani da ido.
"Da su ka yi garkuwa da shi da ɗan sa Isyaku. Sai su ka yi tattaki zuwa maƙabarta inda su ka ɓoye baburan su. Amma ina, ai kuwa sai mutanen ƙauyen nan su ka dake, su ka bi su suna Kabbara.
"Bayan da harsashin ƴan ta'addan ya ƙare, shima kuma Alhaji Nadabo ba zai iya ci gaba da tafiya ba sabo da tsufa, sai su ka kwashe illahirin kuɗaɗen da ke aljihunsa, kimanin dubu 80, sai su ka ranta a na kare," in ji majiyar.
Mai magana da yawun rundunar Ƴan Sanda ta Kano, Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, in da ya ƙara da cewa sun kuɓutar da Sarkin Noman ta haɗin gwiwa da al'ummar garin da kuma ƴan ƙato da gora na yankin.
"Mu na samun rahoton mu ka yi gaggawar tura jami'an mu wajen a daidai ƙarfe 7:57. Da haɗin gwiwar al'umma da ƴan ƙato da gora mu ka samu nasarar kuɓutar da Sarkin. Mu ka kuma daƙile yunƙurin yin garkuwa da shi," in ji Kiyawa.
No comments