Kasar Amurka ta sanya sunan Rasha cikin jerin kasashen duniya dake hana jama’a su gudanar da ’yancin addinin da suke so, yayin da ta cire ...
Kasar
Amurka ta sanya sunan Rasha cikin jerin kasashen duniya dake hana jama’a su
gudanar da ’yancin addinin da suke so, yayin da ta cire sunan Nijeriya da ta
saka a shekarar da ta gabata kamar yadda RFI ta labarto.
Sakataren
harkokin wajen kasar Antony Blinken ya ce ya sanya Rasha cikin jerin kasashen
ne saboda rawar da take takawa wajen tursasawa mabiya wasu addinai da kuma hana
su gudanar da ibadar su kamar yadda suke bukata.
Sauran
kasashen da suke cikin jerin wadanda aka bayyana sun hada da Chana da Myanmar
da Eritrea da Iran da Koriya ta Arewa da Pakistan da Saudi Arebiya da
Tajikistan da kuma Turkmenistan.
Amurkar
ta kuma sanya kasashen Aljeriya da Comoros da Cuba da kuma Nicaragua a cikin
wadanda take sanya ido akan su sakamakon rawar da hukumomin su ke takawa wajen
kin bai wa jama’a ‘yancin gudanar da addinin da suke bukata.
Sakataren
ya sanar da cire sunan Nijeriya daga jerin wadannan kasashe bayan saka ta a
shekarar da ta gabata.
Blinken
ya ce Amurka ba za ta kauda idanun ta daga hakkin da rataya akan ta ba wajen
tabbatar da ‘yancin addini da kuma bai wa jama’a damar gudanar da ibadar su
kamar yadda suke so.
Sakataren
ya ce sun dade suna ganin yadda wasu kasashen duniya ke hantarar jama’a da kama
su da kuma daure su ko cin zarafin su saboda zabin addinin da suke so.
Blinken
yanzu haka ya fara ziyarar wasu kasashen Afirka, inda ya sauka a kasar Kenya,
kafin ya je kasashen Nijeriya da Senegal domin jaddada matsayin gwamnatin
Amurka akan dimokuradiyya da kuma kare hakkin Bil Adama.
No comments