Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Siffofi 10 Na Wani Dan Majalisar Tarayya A Karamar Hukumar Sabon Gari

Daga Fatima Idris Zariya Yayin da aka fara buga gangar siyasa a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna tuni 'ya'yan ...Daga Fatima Idris Zariya

Yayin da aka fara buga gangar siyasa a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna tuni 'ya'yan jam'iyyar APC suka fara fito da wasu halayyar dan majalisar su domin nema masa wani madafar a 2023 .

Honorabul Garba Muhammad Datti Babawo dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna a ma'aunin mabiyansa. Da farko sun fara ne da godewa Allah da ya ba su kalar da suke so.

A don haka ne suka ce a wakilcinsa ne al'ummar Karamar Hukumar Sabon Gari suka fara sanin 'yancinsu a siyasance.

A cewarsu a wakilcinsa ne al'ummar Karamar Hukumar Sabon Gari suka fara sanin mene ne Romon Dimokuradiyya 

A wakilcinsa ne al'ummar Karamar Hukumar Sabon Gari suka fara sanin 'yancinsu ta hanyar yin tsaftatacciyar adawa mai ma'ana a jaridu da mujallu da gidajen talabijin da na rediyo.

A wakilcinsa ne al'ummar karamar Hukumar Sabon Gari suka fara waftar dagwargwajiyar romon dimokuradiyya ta hanyoyi kamar haka;

Na farko samawa matasa da aikin yi domin su dogara da kan su. 

Na biyu Horar da matasa da sana'o'i tare da ba su jari domin su dogara da kan su. 

Na uku samar da wutar lantarki ta hanyar kai wuta garuruwa/anguwanni da sanya wuta mai amfani da hasken rana da samar wa tare da kafa masu tiransifoma. 

Na hudu Samar da ruwan-sha ta hanyar gina rijiyoyin birtsatse da birtsatse mai amfani da hasken rana da kuma samar da babbar janareto ga ma'aikatar ruwa dake Zaria (Zaria Water Board).

Na biyar gina sababbin makarantun Firamare da na Sakandire da karin ginin ajujuwa da sabunta su tare da zuba masu wadatattun kujerun dalibai da na malamai.

Na shida gina asibitocin a matakin farko da yi musu kwaskwarima tare da zuba masu kayan aiki na zamani da gina wurin karbar haihuwa a asibitin A.B.U. dake Tudun Wada da kuma samar da motocin daukar marasa lafiya ga asibitin A.B.U. dake Shika tare da gina Day-Old Theatre Centre duk a asibitin A.B.U. dake Shika, Zariya. 

Na bakwai tura dalibai zuwa kasashen waje domin su karo karatu tare da bai wa daliban gaba da Sakandire tallafin karatu (scholarship) tare raba masu na'ura mai kwakwalwa (Laptop Computer).

Na takwas tura matasa kwararru a harkar kwallon kafa kasashen waje domin samun horon zama kociya.

Na tara yin aikin lafiya kyauta ga talakawa (Free Medical Outreach for Poor) a duk bayan wata uku.

Na goma kyautar motoci da Keke Napep da babura da kekunan dinki da na saka da Janareto da firij da 'deep freezers' ga kungiyo da kuma dai-dai-ku.

Wadannan halaye duk sun kawo su ne a matsayin kalubale ga 'yan adawa da sauran magoya baya.

Tuni dai hasken dan majalisar ke dagawa a cikin lokaci kankani kuma alamu na nuna cewa kwaliyarsa za ta biya kudin sabulu a cewarsu a yayin da mabiyansa ke ganawa da manema labarai a wajan wani taro. 

No comments