Rahotanni daga Filato na cewa an kashe aƙalla mutum 10 tare da ƙone gidaje a wani hari da ƴan bindiga da ba a tantance ba suka k...
Rahotanni daga Filato na cewa an kashe aƙalla mutum 10 tare da ƙone gidaje a wani hari da ƴan bindiga da ba a tantance ba suka kai a Te’egbea ƙaramar hukumar Bassa.
Kwamishinan Watsa Labarai na jihar, Mr Dan Manjang, wanda ya tabbatar wa da BBC da faruwan lamarin ya ce zuwa yanzu ba a tantance adadin hasarar rayuka da dukiya ba.
Wasu rahotanni sun ce an kai harin ne a cikin dare zuwa wayewar safiyar Juma’a inda ƴan bindigar suka buɗe wuta tare da cinna wa gidaje wuta.
No comments