Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum Shida Da Raunata 9 A Katsina

A daren shekaranjiya Juma'a ne 'yan bindiga dauke da manyan bindigogi suka kai hari a garin Gwarjo dake cikin karamar hu...


A daren shekaranjiya Juma'a ne 'yan bindiga dauke da manyan bindigogi suka kai hari a garin Gwarjo dake cikin karamar hukumar Matazu a jihar Katsina, inda suka kashe mutum shida har lahira tare da harbin wasu tara wadanda yanzu haka suna kwance a wasu Asibitocin cikin garin Katsina kamar yadda Katsina Post ta labarto. 

Majiyar Blueink News Hausa ta shaida mata cewa Ƴan bindigar sama da dari dauke da manyan bindigogi, sun shigo garin Gwarjo da Misalin karfe tara na daren shekaranjiya Juma'a har zuwa karfe dayan daren, inda nan take suka fara harbe-harben kan mai uwa-da-wabi har suka kashe mutum shidda har lahira, cikin su wadanda a kashe akwai : Audu Bahillache da Ali Niga da Bello Yusuf da Dan Asibi Ubi da Sanin Ayya da kuma Abdullahi Bello.

Waɗanda kuma suka samu raunuka Daban-daban na harbin bindiga, da suke kwance a asibitin Kashi na Katsina da Asibitin Ƙwararru Ta Gwamnatin Tarayya Dake Katsina da kuma babbar Asibitin Katsina, sun haɗa da Lawal Muhammad da Abubakar Sada da Muhammad Sani da Isiyaku Yahaya, Ma'awiya Dogon Zikiri da Gambo Anas da Buhari Mamman Lada da Ibrahim Garba Dogo da kuma Mamuda Yahaya. 

Akwai kuma Waɗanda suka raunuka Daban-daban a lokacin da suke gudun tsira. Sun kuma kwaci baburan mutane sama da kwara Biyar.

Tuni dai aka yi jana'izar waɗanda su ka rasu su shida a garin Gwarjo dake Karamar Hukumar Matazu kamar yadda Addinin Musulunci Ya Tanada.

No comments