Gwamnatin Sakkwato ta haramta ayyukan ƴan sa-kai a faɗin jihar tare da ƙarfafa aikin ƴan banga. Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Ta...
Gwamnatin Sakkwato ta haramta ayyukan ƴan sa-kai a faɗin jihar tare da ƙarfafa aikin ƴan banga.
Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ne ya sanar da É—aukar matakin a ranar Litinin a wani taron tsaro na jihar, ya ce sha’anin yan sa-kai shi ya Æ™ara haifar da matsala a Zamfara da jihohin da ke maÆ™wabtaka da ita.
Majiyarmu ta BBC ta labarto gwamnan na cewa; suna yin gaban kansu ba tare da bin doka da oda ba. “Ba za mu ci gaba da kyalewa ba domin mun san illar hakan.”
“Mun fito da doka da ta haramta Æ´an sa-kai kuma duk wanda ke son taimakawa jami’an tsaro, to ya shiga aikin banga,” in ji gwamna Tambuwal.
Sanarwar da ofishin gwamnan ta fitar ta ce duk wanda aka kama zai sha É—aurin shekara 14 ko biyan tara ta naira 500,000.
Dokar ta kuma ce duk wanda aka kama da makami a jihar zai sha É—aurin shekara bakwai a gidan yari ko ya biya tarar naira 200,000.
Gwamna Tambuwal ya ce gwamnatinsa ta É—auki matakin ne domin magance matsalolin tsaro da ke damun jihar.
Kuma matakan hanyoyi ne na inganta sha’anin aikin Æ´an banga domin taimakawa jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.
No comments