Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

AN KUMA: 'Yan bindiga Sun Sake Dawowa Hanyar Abuja Zuwa Kaduna, Sun Yi Garkuwa Da Mutane

Daga Muhammad Farouk Masu garkuwa da jama'a sun sake dawowa babhar hanyar Abuja zuwa Kaduna da yammacin yau Litinin, inda su...


Daga Muhammad Farouk

Masu garkuwa da jama'a sun sake dawowa babhar hanyar Abuja zuwa Kaduna da yammacin yau Litinin, inda suka yi garkuwa da gomomin matafiya.  

Masu garkuwa da jama'ar a jiya Lahadi ma sun tare hanyar inda suka sace adadin matafiyan da ba a san yawansu ba tare da kashe wani fitaccen dan siyasar Zamfara, Sagir Hamidu. 

Majiyarmu ta Daily Nigerian ta labarto cewa masu garkuwa da mutanen sun sake dawo wa babban titin Abuja zuwa Kaduna da yammacin yau Litinin da misalin karfe 4:30 inda suka bude masu ababen hawa wuta. 

Lamarin ya auku ne kilomita 5 tsakanin inda harin jiya Lahadi ya auku. 

Lawan Sani, wani ganau da ya bi hanyar ya ce ya ga motoci hudu yashe a kan hanya tayoyinsu a sace.

"Akwai cunkuso da firgici a wurin. Sojoji sun iso wurin da wuri amma 'yan bindigar sun kammala aikinsu cikin 'yan mintoci sun bace zuwa cikin dazuka da mutane da dama da suka yi garkuwa da su", inji Lawan Sani. 

"Na ga mota kirar bas mai fasinjoji 18 mallakin Zamfara, da Toyota Yaris, da Golf Volkswagen da wadansu motocin da ba zan iya tuna kalar su ba. Akwai harsasai a jikin motocin ba tare da masu shi a ciki ba", inji Lawan. 

Mohammed Jalige, Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ba a same shi a waya ba ya zuwa hada rahoton nan. 

No comments