Daga Aqil Abdulkadir A ranar Juma'ar 12 ga watan Nuwamban 2021, Mai Martaba Sarkin Zazzau Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli ya na...
Daga Aqil Abdulkadir
A ranar Juma'ar 12 ga watan Nuwamban 2021, Mai Martaba Sarkin Zazzau Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli ya nada Malam Ahmad Tijjani Ahmad (Khalifa) a matsayin Limamin Kona na Masarautar Zazzau.
Wakilinmu da ya halarci taron ya labarto cewa bikin nadin da aka yi a fadar Zazzau ya tara dimbin masoya na cikin garin Zariya da kewaye wadanda suka zo taya sabon Liman murna.
Kamar yadda aka sani dai LIMAMIN KONA yana cikin mutum 5 dake zaben Sarki a Masarautar Zazzau, har ila yau kuma yana cikin 'yan majlisar Sarki.
Bayan nadin sabon Liman din, ya yi hawa a doki zuwa gidan su gidan Kona dake Limanci Zariya cinda mutane ke ta tururuwar kai masa gaisuwa.
No comments