Shugaban Hukumar Gidajen Yari na kasa, Haliru Nababa Jami'an tsaro tare da masu tsaron gidan gyaran halin garin Jos ...
Shugaban Hukumar Gidajen Yari na kasa, Haliru Nababa
Jami'an tsaro tare da masu tsaron gidan gyaran halin garin Jos a jihar Filato sun rutsa da 'yan bindigar da suka kai farmaki gidan gyaran halin.
Kamar yadda Kakakin Hukumar ne ya sanar da hakan, inda ya ce maharan sun isa wurin ne da misalin karfe 5 na yammaci kuma sun budewa masu tsaron gidan wuta domin su balle shi.
Sai dai sauran cibiyoyin tsaro sun hanzarta kai musu dauki inda suka mamaye gidan kuma suka rutsa da maharan a cikin gidan kamar yadda Kakakin ya ce.
Jeff Longdiem, mai magana da yawun gidan gyaran halin, ya tabbatar da faruwar lamarin a takardar da ya aike wa Daily Trust.
A cewarsa; "Duk da sun samu shiga cikin gidan, a halin yanzu an rutsa da su saboda sauran cibiyoyin tsaro sun gaggauta kawo mana dauki kuma sun mamaye dukkan gidan.
“Sauran cibiyoyin taimakon gaggawa sun hanzarta kawo mana dauki. A halin yanzu komai ya lafa saboda masu ruwan wutan sun ji martanin da ya fi na su daga hukumomin tsaro. Duk abin da ke faruwa za mu sanar da manema labarai," takardar ta ce.
No comments