Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

An Yaba Da Gudummawar Shugaban Jami’ar MAAUN, Farfesa Gwarzo Kan Bunkasar Ilimi A Arewa

Shugaban makarantar koyar da kiwon lafiya ta ‘Arewa Ambassador International College of Health Science and Technology’ dake Zari...



Shugaban makarantar koyar da kiwon lafiya ta ‘Arewa Ambassador International College of Health Science and Technology’ dake Zariya, a Jihar Kaduna, Malam Murtala Iliyasu ya bayyana cewa kafa Jami’ar MAAUN da Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya yi wani abin alfahari ne ga al’ummar yankin arewacin Nijeriya gaba daya.
 
Malam Murtala Iliyasu ya yi wannan bayanin ne jim kadan bayan da ya jagoranci dalibansa a ziyarar da suka kai mazauni na dindin na Jami’ar MAAUN dake GRA Hotoro, a garin Kano ranar Asabar da ta gabata.

Ya kuma kara da cewa, kafa Jami’ar a yankin arewacin Nijeriya ya taimaka wajen samar da kwararru a fannin kimiyya da fasaha.

“Dole mu gode wa Allah a kan kokarin Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, a kan gumunwarsa ga bangaren Ilimi a yankin arewa da ma Nieriya gaba daya,” inji shi.

Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu zai yi wuya a samu wata cibiyar kiwon lafiya a kasar nan da ba za a samu wanda ya kammala karatu daga jami’ar ‘Maryam Abacha American Unibersity of Niger’ ba, tabbas wanna abin alhari ne, muna kuma yi masa fatan alhairi.

Wani jami’i a Jami’ar, Ali Yusuf Kakaki ya zagaya da daliban a ziyarar da suka kai.

No comments