An Yi Jana'izar Dan Siyasar Zamfara Da 'Yan Bindiga Suka Kashe A Hanyar Abuja


An yi jana’izar Alhaji Sagir Hamidu, tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfara wanda ‘yan bindiga suka kashe a hanyar Abuja zuwa Kaduna. 

Jana'izar ta gudana ne a yau Litinin. 

An kashe Alhaji Sagir Hamidu a lokacin da ‘yan bindiga dauke da makamai suka tare hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Lahadi, inda suka yi garkuwa da matafiya da dama.

Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin wadanda suka halarci jana’izar har da Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da kuma tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari.

.         Marigayi Sagiru Hamidu

Post a Comment

0 Comments