Wani mazaunin karamar hukumar mulkin Illela Abdullahi Ghalee, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce: k imanin mutum arba'i...
Wani mazaunin karamar hukumar mulkin Illela Abdullahi Ghalee, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce: kimanin mutum arba'in (40) aka kashe a yayin harin da Æ´an bindiga suka kai garuruwan Kalmalo, Munwadata, Masasa da kuma Runji a cikin karamar hukumar mulkin Illela daren Lahadi zuwa safiyar Litinin. Inda ya ce ya zuwa safiyar ranar Talata akalla mutum 40 din aka yi wa jana'iza.
Ya Æ™ara da cewar: “wannan abin akwai tashin hankali cikinsa, sannan akwai alamar tambaya? Mutanen wannan yanki da abin ya faru da su sun ce suna jin Jirgi na yawo wajen da wadannan mutane suke, sannan wadannan mutane suna zuwa ne akan babura da yawa duk lokacin da wannan jirgi ya sauka cikin wannan daji sai an kawo wa al'ummar yankin hari ko dai su kawo harin a garuruwan dake kusa da dajin, ko kuma wasu kananan hukumomin da ke kusa da wannan daji.
“Abin tambayar shi ne shin gwamnati ta san da wannan jirgi dake sauka da tashi a wannan daji? Sannan su wanene ke cikin wannan jirgi kuma daga ina suke fitowa?
“Saboda abu ne mai wahala a ce mutane sun fito daga dajin Zamfara duk su tsallake kananun hukumomin da ke cikin wannan yanki dake gabashin Sakkwato a ce babu wanda yaga wucewar su", inji shi kamar tadda majiyarmu ta Jaridar Sokoto ta labarto.
Daga ƙarshe ya kuma roki gwamnatin tarayya da kuma ta jihar Sakkwato cewa don Allah su duba wannan koken tare da daukar matakin gaggawa.
“Don Allah Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin jihar Sakkwato ku yi bincike a kai, kuma ku dauki mataki a kan wannan yanki namu na gabashin Sakkwato. Allah ka bamu lafiya da zaman lafiya cikin wannan kasa tamu Nijeriya da jiharmu ta Sakkwato da karamar hukumar mu ta Illela", Inji Abdullahi Ghali.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da hukumomi a jihar Sakkwato ke cewa maharan sun hallaka mutum 12 ne a ƙaramar hukumar mulkin Illela tare da ƙarin mutane 3 a Goronyo zuwa safiyar Litinin, sai dai al'ummar garin na cewa lamarin ya munana domin bayan a adadin da gwamnati ta bayyana da safiyar Litinin ƴan ta'addan sun sake kutsa kai wasu kauyukan da rana tare da yin kisan mai uwa da wabi wanda hakan yasa adadin ya karu zuwa 40.
Tuni dai al'umma a yankin suka bayyana cewa sun riga da sun yi jana'izar mutane 40 kawo yanzu.
No comments