Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

APC Ta Sanya Ranar Zaben Sababbin Shugabaninta Na Kasa

Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta sanya watan Fabarairun shekara mai zuwa a matsayin ranar gudanar da taron ta na kasa wa...Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta sanya watan Fabarairun shekara mai zuwa a matsayin ranar gudanar da taron ta na kasa wanda zai ba ta damar zaben sabbin shugabannin da za su jagorance ta zuwa zabe.

Shugaban Jam’iyyar na riko Mai Mala Buni ya sanar da haka bayan ya jagoranci wasu daga cikin gwamnonin APC ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa.

Masu sanya ido akan siyasar Najeriya na kallon jinkirin a matsayin wani yunkuri na baiwa shugabannin rikon damar warware matsalolin da suka biyo bayan zaben jihohin da akayi, inda APC ta samu shugabanni 92 a jihohi 36.

Rahotanni sun ce shugabannin Jam’iyyar na ci gaba da ganawa da bangarorin da basa ga maciji da juna a jihohin da aka samu matsalolin domin dinke barakar da aka samu kafin zuwa zabe na kasa.
Daga cikin manyan jihohin da Jam’iyyar ke tinkaho da su da aka samu shugabanni guda biyu akwai jihohin Kano da Lagos wadanda ke da matukar tasiri a siyasar kasar.

Yanzu haka wasu daga cikin ’yayan jam’iyyar sun fara korafi akan shugabannin rikon na kasa inda suke bukatar ganin an gaggauta gudanar da taron kasa domin maye gurbin su.

Amma shugaban gwamnonin APC na kasa kuma Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu yace jinkirin da aka samu ya biyo bayan bukatar kammala zabe ne a wasu jihohi guda 4, saboda haka suka bada shawarar dage taron zuwa watan Fabarairu.

 

No comments