Yayin da ake ci gaba da tattara da bayyana sakamakon zaben gwamnan Anambra, bayanai na nuni da cewar dan takarar jam’iyyar APGA ...
Yayin da ake ci gaba da tattara da bayyana sakamakon zaben gwamnan Anambra, bayanai na nuni da cewar dan takarar jam’iyyar APGA mai mulkin jihar kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Farfesa Chukwuma Charles Soludo ke kan gaba wajen samun yawan kuri’u, bayan da ya lashe kananan hukumomi 17 daga cikin 21.
Bayanai sun ce ‘yan takarar da suka hada da Sanata Ifeanyi Uba na jam’iyyar YPP da kuma, Valatine Ozigbo na PDP sun samu nasarar lashe mafi yawan kuri’u a kananan hukumomi guda-guda kowannensu.
Shi kuwa Sanata Andy Uba na jam’iyyar APC bai kai ga samun nasara a karamar hukuma ko da guda ba.
Bayan kidaya mafi akasarin kuri’un da aka kada, dan takarar APGA wato Charles Soludo ya samu kuri’u dubu 99 da 159, Ozigbo na PDP na biye da kuri’u dubu 49 da 475, sai Andy Uba na APC da ya samu kuri’u dubu 40 da 270.
Kimanin ‘yan takara 18 ke fafatawa a zaben gwamnan jihar ta Anambra, wanda hukumar zaben Najeriya INEC ta kara wa’adin gudanarsa daga ranar Asabar zuwa Lahadin nan saboda korafe korafen da aka gabatar kan na’urorin tantance masu kada kuri’a a rumfunan zabe da dama.
Zaben dai ya gudana cikin tsauraran matakan tsaro, inda aka aike da ‘yan sanda akalla dubu 30 domin tabbatar da komai ya gudana cikin kwanciyar hankali.
No comments