Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Ƴar Shekara 18, Aisha Dalil Ta Lashe Gasar Rubutu Ta BBC Hausa

Aisha Dalil, ƴar shekara 18 ce ta lashe gasar rubutu mai taken Hikayata da BBC Hausa ke shiryawa duk shekara. Dalil ta lashe gas...


Aisha Dalil, ƴar shekara 18 ce ta lashe gasar rubutu mai taken Hikayata da BBC Hausa ke shiryawa duk shekara.

Dalil ta lashe gasar ne ta wannan shekarar da labarin da ta rubuta mai taken "Haƙƙina".

A jiya Juma'a da daddare ne a ka sanar da Dalil a matsayin wacce tazo ta ɗaya a bikin kammala gasar da a ka yi a Abuja.

Ta samu kyautar kuɗi ta dalar Amurka 2,000 sannan a ka danƙa mata lambar girma ta nasarar da ta samu a wannan shekarar.

Ƴar shekara 27, Aicha Abdoulaye, ƴar ƙasar Nijer ce ta zo ta biyu a gasar, inda a ka bata kyautar kuɗi, dalar Amurka 1,000 da lambar girma bayan ta rubuta labari mai taken "Butulci".

Zullaihat Alhassan ce ta zo ta uku da labarin da ta rubuta mai taken "Ramat", wanda ke magana a kan haƙƙin masu ƙaramin ƙarfi, inda ta samu dala 500 da lambar girma.

A jawabin da ya yi a taron, Shugaban sashen BBC a Nijeriya, Aliyu Tanko ya ce a bana an samu wadanda su ka shiga gasar daga Kamaru, Sudan, Jamhuriyar Nijer da sauran ƙasashen Afirka.

Ya ce yana fatan labarin da ya lashe gasar ta bana zai zamto maganin matsalolin da ke damun al'umma.

Bayan ya taya waɗanda su ka lashe gasar, Tanko ya kuma haƙurƙurtar da waɗanda ba su samu nasara ba, inda ya ce "ina fatan a baɗi ku ne za ku samu nasarar."

No comments