Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Ba Mu Amince Da Naɗin Pantami A Matsayin Farfesa Ba -ASUU

Kungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa, ASUU ta nisanta kanta daga  naɗin ministan sadarwa, Isa Pantami, a matsayin farfesa a...Kungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa, ASUU ta nisanta kanta daga  naɗin ministan sadarwa, Isa Pantami, a matsayin farfesa a Jami'ar Fasaha ta Tarayya, FUTO da ke Owerri, Jihar Imo.

Ƙungiyar ta ce ba ta gamsu cewa ministan ya cancanci zama Farfesa ba.

Idan za a iya tunawa dai reshen ƙungiyar ta ASUU na jami'ar FUTO ta ce an bi ƙa'idar wajen naɗin Pantami a matsayin farfesa bayan kafa kwamitin bincike.

Sai dai kuma uwar ƙungiyar ta ASUU ta ƙasa ta ce akwai kuskure a naɗin Pantami a matsayin farefsa.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa,  Emmanuel Osodeke ya baiyana hakan a yayin jawabi ga manema labarai bayan taron ƙoli na ƙungiyar a jami'ar Abuja, wanda ya gudana tsakanin ranakun  13 da 14 ga watan Nuwamba.

Osodeke ya ce: Ce-ce-ku-cen da wannan batu ya haifar ba a taɓa samun irinsa a tarihin jami'o'i'n Najeriya.

"Haƙiƙa ya hafar da ka-ce-na-ce tsakanin al'umma na gida da na waje.

"A don haka mun kafa kwamitin bincike kan lamarin," in ji Osodeke.

No comments