A karon farko cikin watanni biyar, za a koma teburin shawara domin farfado da yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran. Ministan harkok...
A karon farko cikin watanni biyar, za a koma teburin shawara domin farfado da yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran.
Ministan harkokin kasashen wajen Iran Saeed Khatibzadeh ya shaida cewa kasar a shiriye take domin cimma matsaya game da farfado da yarjejeniyar, amma tawagar kasar ba za su amincewa Amurka ta shiga tattaunawar ba.
Gwamnatin Iran ta shaida cewa babban fatanta a yayin wannan zama, shi ne cire mata dukkan jerin takunkuman tattalin arzikin da aka kakaba mata.
Ana sa bangaren Firaministan Israila Naftali Bennett ya gargadi shuwagabannin manyan kasashen da za su halarci zaman tattaunawar da su yi taka tsantsana da abin da ya kira kutunguilar Iran.
No comments