Kungiyar Kwadago ta ƙasa, NLC, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi watsi da shirin ƙara farashin man fetur a Nijeriya. Shu...
Kungiyar Kwadago ta ƙasa, NLC, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi watsi da shirin ƙara farashin man fetur a Nijeriya.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Ayuba Wabba ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja a yau Alhamis.
A cewarsa, Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya, NNPC, Mele Kyari, ya sanar da cewa farashin man fetur zai iya yin tashin gwauron zabi har N340 daga watan Fabrairun 2022.
Amma da ya ke maida martani ta sanarwar, Wabba ya bayyana matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na cewa za ta riƙa baiwa ƴan Nijeriya miliyan 40 Naira 5,000 a matsayin abin da zai rage musu raɗaɗin illar karuwar farashin man fetur da cewa babu hikima a ciki.
A cewarsa, jimillar kuɗaɗen da gwamnatin ta ce za ta riƙa bai wa ƴan ƙasa ya zarce kuɗaɗen da ta ce ta na kashewa a halin yanzu kan tallafin man fetur.
Shugaban na NLC ya ce duk wani yunƙuri na kwatanta farashin man fetur a Nijeriya da sauran kasashen duniya zai zama kuskure ne, inda ya siffanta yanayin da cewa "kamar ka kwatanta tuffa da mangwaro ne."
No comments