Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Bafulatani Ba Ɗan Ta'adda Bane -Daga Kwamared Yahaya M. Abdullahi

  Masu karatu ganin halin da muke ciki a wannan yanki namu ko ince a wannan zamanin namu na mayar da al'ummar Fulani kamar s...

 

Masu karatu ganin halin da muke ciki a wannan yanki namu ko ince a wannan zamanin namu na mayar da al'ummar Fulani kamar su ne ƴan ta'adda yasa nace zan ɗan tsakuro wata ƴan muƙala iya nazarina da kuma bincikena akan Fulani da kuma kallon da yau ake musu a wannan nahiya tamu. Idan zamu yi magana dole mu faro daga tushe. 

WANENE BAFULATANI? 

Wasu masu tarihi sun nuna wata ƙungiya ta Fulani sun fito daga ƙasar Sham wato ɗaya daga cikin kasashen Larabawa har suka zo Futatoro suka shigo ƙasar nan a rarrabe. A Wani sashe kuma na masu tarihi suna ƙarfafa cewa, Fulani kabila ɗaya ce, kuma daga tushe ɗaya suke basu da bambanci.

Sun shigo ƙasar Afirika ta ɓangaren yamma wato ta ƙetaren kasashen Larabawa daga wajen ƙasar Masar dai-dai gaɓar kogin Nilu, sai suka bazu a manyan ƙasashen Afirika irin su Mali, Kamerun, Burkina faso, Moroko, Cadi, Gambiya, Muritaniya, Libya, Nijar, Senegal, Aljeriya, Sudan, Kameru, Ghana, Saliyo, Togo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Côte d'Ivoire, Guinea-Bissau da Benin har suka kwararo cikin Nijeriya ta Arewa. A wata fadar kuma an ce, ‘Fulani sun fito daga kasar Sanagal.

Fulani da suka shigo ƙasar Hausa jinsi daya ne, sai dai sun kasu kashi biyu. Akwai Fulanin gida, waɗanda ake wa laƙabi da Fulanin soro sannan akwai masu yawon kiwo a daji masu zaga ƙasa-ƙasa, gari-gari ana musu laƙabi da Fulanin Daji (Makiyaya) 

FULANIN SORO: Waɗanda ake kira da Fulanin Soro Galibinsu dogaye ne, wankan tarwaɗa suke, kuma akan sami farare da baƙaƙe a cikin su, masu kyawawan idanuwa ne da dogayen yatsu na ƙafa da na hannu, galibinsu makaranta Alkur’ani da littattafan tauhidi da sauran littattafan koyarwa na addinin Musulunci ne. 

Sana’arsu kiwo na cikin gida da noma. Halayensu kuwa sun haɗa da kunya, haƙuri, yin liyafa ga baƙi, iya jagorancin jama’a. Fulanin gida ne kuma suka raya addinina Musulunci a Arewacin Nijeriya harma suka miƙa shi wani sassa na yankin Yarbawa, wato zamanin Jihadin Shehu Usmanu ɗan Fodio Bafulatanin daya tabbatar da addini a nahiyar Afrika baki ɗaya. 

FULANIN DAJI (MAKIYAYA)

 Yawancinsu farare ne fat, kuma kyawawan gaske kamar Larabawa, wasu kuwa wankan tarwadane, amma akan sami baƙaƙe kadan a cikin su.

Suna da yawan gashi, mazansu da matansu. Fulanin daji ne suka fi wauta da jarunta, ga su da karfin hali da dauriya gami da juriya ga dukkan abunda suka sa a gaba.

Sana’arsu kiwon dabbobi da saƙa irin ta kaba. Al’adarsu kuwa yawan tashi daga wannan wuri zuwa wancan suna tafe suna ta bushe-bushen sarewa, suna nema wa dabbobinsu abinci. Sukan zagaya kasashen da ake samun ciyawa a bakin kogi musamman lokacin rani. Basa son zama a cikin gari sai dole, kai koda ya zama dolenma sukan so inda ya fi kusa da daji domin dashi suka saba. 

Sukan shiga gari ne kawai don sayen kayan masarufi, shima sai in ya zama dole domin cikin gari yakan zame musu tamkar abun tsoro ne domin gudun duniya, a haka suke rayuwarsu cikin jarumta a wannan dajin.

A yau an wani yari waɗannan Fulani na Daji da aka sani da Noma da Kiwo wasu Ƙabilu (Haɓe) sun tarar dasu a inda suke wannan kiwo da noma sun basu bindiga da alburusai suna amfani dasu wajen ƙarfafa sana'ar kasuwancinsu, abunda yasa na kira shi da kasuwanci saboda a yanzu abubuwan ake aikatawa a arewa ba komai bane face kasuwanci mai ɗimbin riba, kawai jarin da ake zubawa shine shiga daji da tara Fulanin da basu da yawo suyi suyi maka aiki, kai kuma a cikin gari kana zaune sai ka dinga zuwa lokaci-lokaci kana karɓan Ribar da aka samu sai kuma a siyo kayan aiki, su kam ko dubu goma ka basu karɓa zasuyi domin basu ma san me zasu yi da kuɗin ba idan ka basu tunda su basu san komai ba sai rayuwarsu ƙarƙashin Kargo da Sabara.

Kwanakin baya na ci karo da wani yaron Fulani ƙarami ana masa tambaya saboda ganin sigari(taba) a hanunsa aka ce masa yana shan giya yace sai ta leda kawai yake sha, da sigarinsa, aka ce baya azumi yace baya yi, sai aka ce masa shi Musulmi ne? Sai yace shi Fulani ne kawai, to irin waɗannan yaran ne suke siya tunda su komai zasu iya aikatawa a cikin birni domin su samu kuɗi, sai su basu makamai su ce musu kashe mutane shine addini da sace mutane, shi kuma ya samu sana'a da kuma hanyar tsira a Lahira shike nan.

To a yanzu ma zaka samu an kama mutane da daman gaske dake aikata wannan mummunan aikin zaka samu ba Fulani bane domin kowa ma yana iya muryan Fulani ai matuƙar in yana so ya biya wata buƙatarsa musamman ɗan Najeriya da ya yarda da kuɗi fiye da uwar data Haifeshi. Akan kama mutane da yawan gaske ba Fulani bane kawai rigar Fulanin suke saka waw domin cimma muradinsu na karɓan kuɗin fansa a gurin wanda suke so sai ace Fulani, kwanaki ma har Soja an kama da wannan aikin, ana kama Igbo, Yarbawa, musamman Hausawa da sauran yaren dake kusa dasu, to amma Meyasa Fulani kawai?

Shin ƴan Najeriya mun Taɓa karatun Tanutsu akan abubuwan nan da suke addabarmu, in mun yi mene ne mafita?

Kwamared Yahaya M. Abdullahi, Ɗan Jarida, Marubuci. Za a iya samunsa ta 07033800660 ko a Comradeyahayamabdullahi@gmail.com

No comments