Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Bakar Rana Ga Ganduje: Kotu Ta Rushe Shugabancin Abdullahi Abbas

                  Gwamna Ganduje Daga Wakilinmu Kotun daukaka kara a Nijeriya ta amince da zaben shugabannin Jam’iyyar APC na Ji...

                  Gwamna Ganduje

Daga Wakilinmu

Kotun daukaka kara a Nijeriya ta amince da zaben shugabannin Jam’iyyar APC na Jihar Kano bangaren Malam Ibrahim Shekarau wanda ke karkashin jagorancin Alhaji Haruna Ahmadu Danzago, yayin da ta yi watsi da bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

.         Alhaji Haruna Ahmadu Danzago


Alkalin kotun daukaka kara dake Abuja Hamza Mu’azu ya yanke hukuncin amincewa da bangaren tsohon gwamnan sakamakon karar da ya shigar inda yake kalubalantar halarcin bangaren gwamnan mai ci wanda aka zabi Alhaji Abdullahi Abbas.

.                   Abdullahi Abbas

Wannan ya biyo bayan tarurrukan jam’iyyar guda biyu da aka yi a birnin Kano a ranar 16 ga watan Oktoba wanda Gwamna Ganduje da tsohon Gwamna Shekarau suka jagoranta a wurare daban daban.

Kwamitin kula da kararrakin zabe na Jam’iyyar APC ya amince da bangaren Gwamna Ganduje wanda aka zabi Abdullahi Abbas, yayin da bangaren Malam Shekarau ya ruga kotu domin neman hakkkin su.

Rikicin cikin gida na nema jefa jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya cikin mummunar yanayi a daidai lokacin da ake tunkarar zaben shekarar 2023.

Rahotanni sun ce lokacin gudanar da taron Jam’iyyar da aka yi a jihohin kasar 36 an samu rarrabuwar kawuna a jihohi da dama cikin su harda jihar Kano da Legas inda aka gudanar da tarurruka bibbiyu da kuma samun shugabanni bibbiyu a jihohin wadanda ke da matukar tasiri ga jam’iyyar.

Wannan na daga cikin matsalolin da suka hana Jam’iyyar gudanar da taron ta na kasa domin zabo shugabannin da za su jagorance ta a matakin kasa.

Ko a makon jiya, shugaban jam’iyyar na riko Mai Mala Buni da shugaban gwamnonin APC Atiku Bagudu da Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari game da halin da jam’iyyar ke ciki da kuma shirin taron ta na kasa, inda suka yanke hukuncin sanya watan Fabarairu mai zuwa a matsayin lokacin taron.

.                   Mai Mala Buni

Gwamna Bagudu ya ce za su yi amfani da lokacin da suke da shi kafin watan Fabarairun domin warware matsalolin cikin gidan da suka shafi zaben jihohin da ake rikici akan su.


A wani labarin kuma, wata kotu a birnin Tarayya Abuja ta yanke hukuncin cewar dauke tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II daga Kano zuwa Nasarawa bayan tube shi daga karagar mulki a ranar 12 ga watan Maris na shekarar 2020 ya saba ka’ida.


Alkalin kotun Anwuli Chikere yayin yanke hukuncin ya ce dokar Majalisar Masarautar ta shekarar 2019 da gwamnatin Jihar Kano ta yi amfani da ita wajen kai Sarki Sanusi Jihar Nasarawa ya sabawa kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999.

Chikere ya ce kundin tsarin mulkin Nijeriya ya fi karfin duk wata doka da aka yi, saboda haka tsohon Sarkin na da hurumin zama inda yake so a Nijeriya ciki harda jihar Kano kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba shi dama.

Kotun ta bai wa gwamnatin jihar Kano da Sufeto Janar na ‘yan Sandan Nijeriya da Darakta Janar na Hukumar DSS umurnin biyan diyyar naira miliyan 10 da kuma neman gafarar tsohon Sarkin a cikin manyan jaridun kasar guda 2.

Sarki Sanusi ya shigar da karar ne inda ya bukaci kotu da ta haramta tsare shi da aka yi wanda ya sabawa 'yancinsa da kuma dauke shi daga Kano.

Wannan ya biyo bayan sauke shi daga karagar mulki a matsayin Sarkin Kano na 14 da gwamnatin jihar Kano a karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta yi, inda ta maye gurbinsa da Sarki Aminu Ado Bayero.

Sarki Sanusi bai kalubalanci sauke shi daga karagar mulki da gwamnatin jihar Kano ta yi a gaban kotun ba, kuma ita ma kotun ba ta ce komai akan raba shi da sarautar ba.

No comments