Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Budurwar Da Aka Kama Da Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi A Saudiyya Ta Zama Ma'aikaciyar NDLEA

Zainab Aliyu, matashiyar nan da a shekarar 2019 ta shafe watanni a tsare a kurkukun Saudiyya bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi...


Zainab Aliyu, matashiyar nan da a shekarar 2019 ta shafe watanni a tsare a kurkukun Saudiyya bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi, ta zama jami'ar hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya, NDLEA.

An sako Zainab ne daga kurkukun Saudiyya a ranar 30 ga watan Afrilun 2019 bayan an gano cewa ba ta da laifi wasu ne suka yi mata sharri.


A yanzu matashiyar, mai shekara 25, ta kammala karɓar horo a Kwalejin horas da jami'an hukumar ta NDLEA da ke Katon Rikkos a jihar Filato da ke Nijeriya.

Bayan kammala karɓar horon, ta fito da anini ɗaya a matsayin 'Assistant Superintendent of Narcotics'.

Ta shaida wa BBC cewa irin ƙaddarar rayuwar da ta faru da ita ce ta ja ra'ayinta shiga wannan aiki na yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi.

"Abin da ya faru da ni a 2018 ya sauya min rayuwata har abada kuma ya sa na zama jami'ar NDLEA domin na bayar da gudunmawa wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Nijeriya.

"An yi kuskure wajen zargin da aka yi mani da safarar miyagun ƙwayoyi, ganin cewa na fara aiki a yanzu, zan tabbatar da cewa an rinƙa gudanar da bincike sosai don kada a kama mutumin da ba shi da laifi."

Zainab, wadda ta kammala karatun digirinta daga Jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano ta taɓa zama muhimmin batu a Nijeriya a lokacin da ake ta fafutikar ganin an sako ta.

Zainab ta shafe watanni huɗu a gidan yarin Jeddah a inda a nan ne aka yanke mata hukuncin kisa, bayan nan ne hukumomin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin ministan shari'a Abubakar Malami suka yi ƙoƙarin ganin an sako ta.


Daga baya hukumar NDLEA ta kama wasu ma'aikata a filin jirgin Malam Aminu Kano da ke Kano waɗanda su ne ake zargi da saka mata ƙwayoyin a cikin kayanta haka kuma ba ta san an saka mata ƙwayoyin ba har sai bayan da aka kamata.

Mahaifinta Habib Aliyu ya yi godiya ga Allah bayan ƴarsa ta samu wannan aiki da Hukumar NDLEA a yayin wata hira da BBC.

Hakazalika ƴar uwarta Hajara ita ma ta shaida cewa suna matuƙar alfahari da Zainab bisa wannan mataki da ta kai a yanzu.

Sai dai a yayin yaye sabbin jami'an hukumar ta NDLEA wanda aka yi a jihar Filato a ranar Juma'a, shugaban hukumar Buba Marwa ya yi gargaɗi ga sabbin jami'an kusan su 2,000 da kada su yarda masu safarar miyagun ƙwayoyi su yaudare su da kuɗi su kuma tabbatar sun yi aikin su yadda ya kamata.

Yadda aka kama Zainab a 2018

Zainab ta je Saudiyya ne domin aikin Umrah amma ba ta samun damar yin aikin ba sakamakon a ranar da ta isa aka kamata.

An kama Zainab ne a birnin Madina a gaban mahaifiyarta da kuma ƴar uwarta a cikin Otel ɗin da suke zaune. Jami'an ƙasar sun shiga har ɗaki inda suka shaida musu cewa sun ga ƙwayoyi a cikin wata jaka wadda lambar jakar ta zo ɗaya da lambar fasfo ɗinta wanda hakan ya sa suka tafi da ita.

Yar uwarta Hajara Habib ta shaida wa BBC cewa a lokacin da lamarin ya faru, suna magana da Zainab kusan kullum sakamakon tana amfani da wayar gidan fursuna domin su yi magana.

"Wani lokacin za ta kasance cikin ɓacin rai, da kaɗaici da damuwa.

"Wani lokaci kuma za ka ji ta da kuzari idan muka ba ta ƙarin bayani dangane da halin da ake ciki da batun ta," in ji Hajara ƴar uwarta.

Daga baya hukumomin Nijeriya suka kama mutum bakwai waɗanda suke zargi da saka wa Zainab ƙwayoyi a cikin jakarta.

Ƙasar Saudiyya dai ba ta ɗaukar lamarin safarar miyagun ƙwayoyi da wasa, inda aksarin waɗanda aka kama da laifin ana aiwatar musu da hukuncin kisa ne.

Wace ce Zainab Aliyu

An haife ta ne a cikin garin Kano da ke arewacin Nijeriya a shekarar 1996.

Ta yi makarantar firamare da sakandare a Essence College da ke cikin garin Kano.

Bayan ta kammala makarantar sakandire a 2014, sai ta samu gurbin karatu a Jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano.

Zainab na daf da kammala jami'a ne ta haɗu da wannan mummunar ƙaddara amma ta samu ta kammala jami'ar a 2019 bayan an sako ta.


-Rahoton BBC 

No comments