Buhari Ya Taya Soludo Murnar Lashe Zaben Gwamnan Anambra

 


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Charles Chukwuma Soludo na jam'iyyar APGA lashe zaben jihar Anambra da aka gudanar a karshen makon jiya.

A wata sanarwa da Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar ranar Laraba, ya bukaci sabon gwamnan da ya hada kan masu ruwa da tsaki a jihar domin shawo kan matsalolin da ke addabarta da ma yankin Kudu maso Gabas.

"Shugaban kasa yana sa ran aiki da gwamna mai jiran gado domin tattabar da zaman lafiya da tsaro da kuma samar da ci gaba ba kawai a jihar Anambra ba, har ma da kasa baki daya," in ji sanarwar.

Shugaba Buhari ya kuma jinjina wa jami'an tsaro wajen ganin sun tabbatar da an gudanar da zaben jihar cikin lumana.

Soludo ya yi nasara a zaben ne inda ya samu kuri'a 112,229.

Post a Comment

0 Comments