Mutum akalla 57 ‘yan bindigan Daji suka kashe a jihar Sakkwato a cikin kwanaki biyu da suka gabata. Bayanai na nuna da cewa a karamar Huku...
Mutum
akalla 57 ‘yan bindigan Daji suka kashe a jihar Sakkwato a cikin kwanaki biyu
da suka gabata.
Bayanai
na nuna da cewa a karamar Hukumar Goronyo mutum
43 aka kashe sai kuma mutum 14 a yankunan Sabon Birni duk dai a Jihar ta
Sakkwato.
Harin
na zuwa ne jim kadan bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci a kara
tura sojoji yankin domin a murkushe ‘yan bindigar dajin da suka hana sukuni a
yankin.
Wani
mazaunin yankin wanda ya gaskata harin ya bayyana cewa ‘yan bindigar dajin sun
mamaye kauyuka dake yankin Unguwar Lalle tun daren Talata inda suke ta ayyukan ta’addanci.
Gwamnan
Jihar Sakkwato Aminu Tambuwal ya fadi cewa suna ci gaba da kokarin kawo karshen
hare-haren.
Kwamishinan
‘yan Sandan jihar Kamaludeen Okunlola ya gaskata hare-haren da aka kai inda ya
ce suna iyakacin kokarin kama ‘yan bindigar kamar yadda majiyarmu ta labarto mana.
No comments