Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Da Yiwuwar Farashin Man Fetur Ya Kai Naira 340 A 2022, Inji NNPC

Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Mele Kyari ya ce akwai yiwuwar farashin man fetur ya kai Naira 340 a shekarar 2022. Mele K...



Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Mele Kyari ya ce akwai yiwuwar farashin man fetur ya kai Naira 340 a shekarar 2022. Mele Kyari ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a taron Bankin Duniya kan ci gaban Nijeriya na watan Nuwamba a Abuja a ranar Talata.

Mele Kyari ya ce tabbas za a cire tallafin man fetur a cikin shekara mai zuwa, kamar yadda doka ta tanada.

“Babu wata doka da za ta tanadi ci gaba da biyan tallafin man fetur, amma na tabbatar za ku yaba wa tsare-tsaren da gwamnati za ta bullo da su domin jin dadin jama’a, da nufin ganin talakawa ba su sha wahala ba,” inji shi kamar yadda majiyarmu ta Jaridar Daily Trust ta labarto. 

A kan batun hauhawar farashin iskar gas kuwa, Shugaban na NNPC ya alakanta hakan da tsanantar bukatar yawan makamashin a fadin duniya, inda ya ce yanzu haka kasashe da dama na fuskantar karancinsa.

Mele Kyari ya ce farashin na yin tashin gwauron zabo ne saboda babu tallafin gwamnati a cikinsa, sabanin a man fetur.

Sai dai ya ce NNPC na aiki tukuru wajen ganin ya samar da wadataccen makamashin na iskar gas.

No comments