Daga Karshe An Bizne Birgediya Janar Zirkushu Da Sojoji 6 Da Ƴan ISWAP Suka Kashe


Ani bizne Birgediya Janar Dzarma Kennedy Zirkushu tare da wasu sojoji shida da ƙungiyar ISWAP ta kashe a farkon watan nan a jihar Borno. 

Rahotanni sun ce an bizne su ne a wata maƙabartar sojoji da ke Yola ta jihar Adamawa.

Gwamnan jihar na Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya bai wa iyalan janar ɗin kyautar naira miliyan 10 da kuma saka wa wani sanannen titi a Yolan sunan janar ɗin.

Kazalika ya bai wa iyalan sauran sojoji shidan naira miliyan 17.

Post a Comment

0 Comments