Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Daliban Islamiyya Da Dama Sun Mutu A Hatsarin Kwale-kwale A Hanyarsu Ta Zuwa Maulidi A Jihar Kano

Rahotanni daga jihar Kwano sun nuna cewa mutane da dama ciki har da daliban Islamiyya ne suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwal...


Rahotanni daga jihar Kwano sun nuna cewa mutane da dama ciki har da daliban Islamiyya ne suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Bagwai.

Rahotannin sun nuna cewa fiye da mutum 30 ne suka bata bayan hatsarin kwale-kwalen da yammacin ranar Talata.

Bayanai sun nuna cewa mutanen sun taso ne daga kauyen Badau zuwa garin Bagwai domin yin maulidi amma kwale-kwalen ya nutse da su.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Kano ta tabbatar wa BBC Hausa faruwar lamarin, tana mai cewa kwale-kwalen yana dauke da mutum kusan 50.

Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa wakilinmu na Kano, Khalifa Shehu Dokaji, cewa "kwale-kwalen mai dauke da kusan mutum hamsin ya kife a kogin Bagwai.

"Ya zuwa yanzu mun gano gawar mutum ashirin, sai kuma mutum bakwai da aka ciro da ransu sanna ana ci gaba da neman wasu da dama da suka nutse."

Ganau sun shaida mana cewa jirgin ya nutse ne a kogin Bagwai sakamakon daukar mutane fiye da kima.

Hatsarin kwale-kwale ba wani sabon abu ba ne a Nijeriya lamarin da yake matukar tayar da hankalin mutane saboda rashin daukar matakin dakile shi.

-(BBC)

No comments