Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dan Tsohon Shugaban Libya Gaddafi Ya Yi Rijistar Takarar Zaben Disamba

Saif al-Islam al-Gadhafi, mai shekaru 49, ya bayyana ne a cikin wani faifan bidiyo na hukumar zaben sanye da riga mai launin ruw...


Saif al-Islam al-Gadhafi, mai shekaru 49, ya bayyana ne a cikin wani faifan bidiyo na hukumar zaben sanye da riga mai launin ruwan kasa da rawani, kuma da farin gemu da gilashi, yayin da ya sanya hannu a kan takardu a cibiyar zabe a garin Sebha da ke kudancin kasar.

Saif al-Islam al-Gadhafi na daya daga cikin fitattun mutane kuma mai yawan cece-kuce wadanda ake sa ran za su tsaya takarar shugaban kasa, sauran jerin sunayen sun hada da Kwamandan sojojin gabashin kasar Khalifa Haftar, da Firaminista Abdulhamid al-Dbeibah da kuma Kakakin majalisar dokokin kasar Aguila Saleh.

Sai dai kuma duk da cewa sunansa na daya daga cikin fitattun mutane a kasar Libya, kuma ko da yake ya taba taka rawar gani wajen tsara manufofin da kungiyar tsaro ta NATO ke marawa baya a shekara ta 2011, wanda ya ruguza gwamnatin iyalansa, da kyar ake ganinsa cikin tsawon shekaru goma da suka gabata.

Wani babban taro da aka yi a birnin Paris ranar Juma'a ya amince da sanya takunkumi ga duk wanda ya kawo cikas ko hana zaben, amma yayin da ya rage kasa da makonni shida a kammala zaben, har yanzu ba a cimma matsaya kan dokokin da za su iya tsayawa takara ba.


No comments