Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Duk Da Alkawarin Gwamna, Har Yanzu Ba A Dawo Da Sadarwa A Sauran Kananan Hukumomin Zamfara Ba

Daga Wakilinmu Duk da alkawarin da Gwamnan jihar Zamfara, Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun ya yi na tabbatar da cewa daga ji...


Daga Wakilinmu

Duk da alkawarin da Gwamnan jihar Zamfara, Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun ya yi na tabbatar da cewa daga jiya Litinin zuwa yau Talata za a bude sadarwa a dukkanin kafatanin sauran kananan Hukumomin jihar tare da sauran kasuwanni da aka kulle domin kowa ya ci gaba da walwalarsa. 

Idan ba ku manta ba, a ranar 4 ga watan Satumban 2021 ne dai aka toshe hanyoyin sadarwa a wasu sassa na jihar a kokarin da ake yi na yaki da ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran ’yan ta’addan da suka addabi Jihar.

Sai dai a watan da ya gabata, aka dawo da hanyoyin sadarwar a Gusau, babban birnin Jihar.

Da yake jawabi ranar Asabar, jim kadan da kammala zaben shugabannin jam’iyyar APC a matakin Jihar, Gwamna Matawalle ya ce za a dawo da hanyoyin sadarwar tare da dage haramcin cin kasuwannin mako-mako a Jihar.

A cewarsa, “Daga bayanan da muka samu, an samu ci gaba matuka wajen yaki da ayyukan ’yan ta’adda a Jiharmu. Saboda haka, nan da ranar Litinin ko Talata, mutanen wadannan yankunan za su samu damar yin mu’amala da ’yan uwansu ta waya.

Sai dai wakilinmu da ya tuntubi mazauna jihar Zamfarar musamman wadanda suke zaune a Gusau, sun ce lallai har yanzu ba a iya samun mazauna sauran kananan hukumomin da aka datse sadarwar. Wanda hakan ke nuni da cewa idan yau Talata ta wuce ba a dawo da sadarwar ba, gwamnatin jihar ba ta cika alkawari ba. 

No comments