Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Duk Kwakwalwar Da Ta Samar Da Jami’ar MAAUN Kano Jarumi Ne Mai Kishin Ilimi –Dr Sani Jauro, Shugaban Jami’ar Pen Resource Gombe

Dr Sani Jauro, shugaban Jami’ar Pen Resource da ake son kafawa a Gombe ya bayyana cewa duk kwakwalwar da ta samar da Jami’ar Mar...


Dr Sani Jauro, shugaban Jami’ar Pen Resource da ake son kafawa a Gombe ya bayyana cewa duk kwakwalwar da ta samar da Jami’ar Maryam Abacha American University dake Kano, lallai mutum ne jarumi mai kishin ilimi.

Dr Jauro ya bayyana hakan ne a ziyarar da ya kai wa Jami’ar ta Maryam Abacha American University dake Nijeriya a Kano inda ya samu kyakkyawan tarba daga  Alhaji Lawal Abubakar Kankiya, daya daga cikin jami'an ya kuma kewaya da shi dakunan karatu da gwaje-gwajen ilimin kimiyya. 


Dr Jauro tunda fari ya bayyana jindadinsa bisa yadda ya ga gine-ginen Jami’ar ta MAAUN Kano, inda ya bayyana makasudin ziyararsa da cewa; “dalilin  zuwana wannan Jami’ar shi ne ina zagayawa ina ganin Jami’o’i irin wadannan wadanda aka riga aka kaddamar domin mu ga irin abin da ake yi mu ma mu yi koyi daga wadanda suke gaba da mu. Aka ce da na gaba ake gane zurfin ruwa. Alhamdulillah na zo wannan jami’ar, kuma abin da na gani ya burge ni matuka. Duk yawon da na yi, na je jami’o’i da yawa, amma ban ga jami’ar da ta ginu, babu ganda ga kishi, an zuba kudi an yi abin da ya dace kamar wannan ba (Jami’ar MAAUN)”, inji shi.

Ya ci gaba da cewa; “duk kwakwalwar da ya haifar da wannan Jami’a na mutum ne jarumi mai kishin ilimi, wanda ba ya kyashin ya kashe kudinsa don saboda abin da ya dace wanda zai raya ilimi”, ya jaddada.

“a don haka muna alfahari da wadanda suka yi wannan Jami’ar, kuma muna fatan Allah ya karo musu budi, kuma Allah ya daukaki wannan Jami’ar ta kai duk matakin da ba a tsammani”, ya yi kyakkyawan fata.

Da yake bai wa Farfesa Gwarzo shawara dangane da wannan Jami’ar, Dr Jauro ya ce; ya san dai Farfesa Gwarzo ya dade a cikin Harkar ilimi na Jami’a tunda yana da Maryam Abacha American University na Jamhuriyyar kasar Nijer, inda ya kara da cewa; “Saboda haka wannan ba shi ne na farko da yake yi ba. Saboda haka dagewarsa a cikin wannan Harka ya tabbata. Ina kira gare shi ya kara kaimi ya kara dagewa ya ci gaba da bunkasa wannan Jami’a, domin kusan ba wani abu da zaka yi ka bar baya a kasar nan da ya wuce ka samar da Jami’a, ko kuma ka samar da makarantu na koyon ilimi ko na boko ne ko na addini. Saboda haka ina kira a gare shi wannan hanya da ya dauka hanya ce sahihi kuma ya kara dagewa ya kara riko gare shi ya kara azama ya kara zuba dukiyarsa a ciki”.

Dr Sani Jauro ya yi kira gwamnatin Tarayya, da ta taimaka ta samar da Bankin Raya Ilimi domin bunkasa ilimi a kasarnan kamar yadda ta samar da bankunan raya noma da na masana’antu, inda ya ce samar da jami’o’i masu zaman kansu akwai matukar wahalan gaske.

“samar da jami’o’i masu zaman kansu a kasarnan, abu ne mai wahalan gaske. Kuma babu wani abu da yake zuwa daga gwamnati a iyakacin sani na. Idan ka tashi za ka samar da jami’a sai dai ka dage ka runtse ido ka je ka ci bashi a banki. Mu mun sani cewa cikin ayyukan gwamnati akwai taimakawa wurin raya al’amuran rayuwa na dan Adam. Misali akwai Bankin raya manoma, akwai bankin raya masana’antu, to mu abin da muke kira ga gwamnati ta yi Bankin raya ilimi; yadda ba jami’o’i kawai ba, da Firamare, da nasari, da Sakandare da jami’o’i, duka za su iya zuwa su ci bashi a wurin, ya zama ribar da gwamnati za ta samu ko kuma ita bankin za ta samu ba mai wahalarwa bane. Misali a ce kashi 5 ko 9 ma da ake bai wa bangaren noma. Ina ga idan gwamnati ta yi haka za ta taimaka wajen bunkasa ilimi”, inji shi.

Ya ci gaba da cewa; “Babu wata kasar da ta taba ci gaba ba tare da riko da ilimin mutanen kasar ta ba. Domin ka ce ka yi Bankunan manoma, ka yi na masana’antu, ya za a yi a raya harkar noma da masana’antu idan babu ilimi?”, Dr Sani Jauro ya tambaya.

“ni ina kira ga gwamnatin Tarayya ta yi Bankin ilimi ko kuma ta yi wata kafa wanda za a iya samu a samu kudi cikin sauki domin a raya ilimi. Ba a ce a bayar kyauta ba. A bayar bashi amma ruwan ya zama ba mai yawa bane. Yadda mutane za su iya dauka kuma su bunkasa harkar ilimi din nan. Idan ya so idan an yi hakan, sai a kawo ka’idoji, kuma a tsaya a dage akan wadannan ka’idoji kuma kowa sai ya bi wadannan ka’idoji din saboda samun ilimi mai inganci”, ya nusasshe.

Ya yi fatan daliban da za su shiga wadannan jami’o’i masu zaman kansu Allah ya ba su ilimi mai inganci, inda yake cewa; “muna fatan Allah ya ba su ilimi mai inganci, wanda zai zama sanadin kubutar su a nan duniya da gobe kiyama. Kuma ya zama mai amfani ga mutanen Nijeriya da duniya baki daya”, ya karkare.

No comments