Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

El-Rufai Ya Sake La’antar Sanata Shehu Sani Da Hunkuyi

  Daga Muhammad Farouk  Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya sake jaddada tsinuwa da la’anta ga tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanat...

 

Daga Muhammad Farouk 

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya sake jaddada tsinuwa da la’anta ga tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani da tsohon Sanatan shiyya ta daya a jihar Kaduna, Sanata Suleiman Hunkuyi bisa abin da ya kira cewa su makiyan jihar Kaduna ne domin a cewar gwamnan sun hana shi ciwon bashin da zai yi wa ‘yan jihar aiki da shi. 

Har wala yau gwamnan ya yi amfani da wannan damar wajen rokar al’ummar jihar ta Kaduna da ka da su sake su zabi jam’iyyar PDP a zaben da za a yi a shekarar 2023 mai zuwa.

El-Rufai ya yi zargin cewa idan ba don halin ja-in-ja da tsohon Sanata Shehu Sani da Suleiman Hunkuyi suka yi da shi ba, da ci gaban jihar Kaduna ya zarce irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu wanda a yanzu mutanen Kaduna ke ta murna a cewarsa.

A cewarsa, matakin da Shehu Sani da Suleiman Hunkuyi suka dauka ya kawo koma baya ga ci gaban a jihar, inda ya nuna cewa a shekarar 2023 ya kamata jama’a su yi hattara da wanda za su kada wa kuri’a domin kaucewa kawo wasu makiya jihar Kaduna da ya kamata a la’anta a cewarsa.

"Shehu Sani da Hunkuyi tsinannu ne," El-Rufai a fusace, inda jama’a suka amsa masa da “Amin’ cikin daga murya mai karfi.

El-Rufai dai ya fadi hakan ne a cikin dakin motsa jiki na ‘Ahmadu Bello Stadium' inda daruruwan jama'a suka yi dafifi domin kaddamar da sabon tsarin kudi a jihar.

El-Rufai ya ce idan suka zabi PDP to za su mayar da Nijeriya cikin matsalolin da suka wuce.

Ya ce ya kamata jama’a su yi gangami su zabi wanda zai nada a matsayin Gwamnan Jihar a 2023. Gwamnan ya shawarci al’ummar Kaduna da su amince da shi a zabin da zai yi musu.

Ya bayyana gadar Kawo ta zamani da ya yi wanda ya kammala da cewa; bai kamata a ba shi ladar aikin shi kadai ba, domin a cewarsa ‘yan majalisar jihar sun cancanci yabo domin yadda suka tabbatar da cewa aikin ya samu goyon bayan majalisa, da kuma jama’ar jihar Kaduna da ke goyon bayan gwamnatinsa.


No comments