Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Farfesa Abubakar Gwarzo, Abin Alfahari Ne Ga ’Yan Afirka —Kasimu Audu Bakori

Wani Malami a Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Kaduna, Kasimu Audu Bakori ya bayyana cewa wanda ya kafa Jami’o'in Maryam Abacha...


Wani Malami a Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Kaduna, Kasimu Audu Bakori ya bayyana cewa wanda ya kafa Jami’o'in Maryam Abacha American University (MAAUN) da Franco-British International University (FBIU) a Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo abin alfahari ne ga daukacin ‘yan Afirka duba da jajircewarsa wajen bunkasa ilimi.

Ya bayyana hakan ne a kwanan nan a lokacin da ya jagoranci wasu dalibai daga sashen yawon bude ido inda suka ziyarci muhallin dindindin na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya dake Kano.

Malamin ya yabawa Farfesa Abubakar Gwarzo bisa kafa jami'ar tare da samar da kayan aikin fasahar zamani domin koyar da ingantaccen ilimi. 

"Maganar gaskiya abin da na gani a Jami’ar (MAAUN) ya tabbatar min da cewa zai yi wahala a samu wani mutum mai himma wajen bunkasa harkar ilimi irin Farfesa Abubakar Gwarzo. 

"A don haka, ya kamata ya zama babban abin alfahari ga dukkan 'yan Afirka a duk inda suke a fadin duniya," in ji shi.

A bisa haka Bakori ya yi kira ga masu hannu da shuni musamman a Nijeriya da ma nahiyar Afirka baki daya da su yi koyi da Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ta hanyar kafa irin wadannan cibiyoyi domin bai wa matasa damar samun ingantaccen ilimi domin ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin nahiyar.

Daya daga cikin jami’anta Kwamared Ali Yusuf Kakaki ne ya zagaya da daliban da suka ziyarci jami’ar.

Daga cikin wuraren da aka ziyarta sun hada da manyan ajujuwan daukar karatu, dakunan gwaje-gwaje, Tsangayar harkokin shari'a, dakin karatu da kuma karamin rukunin wasanni na jami'ar.

Daya daga cikin daliban, Ashiru Shitu wanda ya yi magana a madadin takwarorinsa dalibai ya bayyana farin cikinsa kan yadda ya gani tare da kuma yadda aka sanya kayayyakin fasaha a makarantar.

A don haka ya shawarci matasan da suke da takardar shaidar kammala karatu kuma suke da burin ci gaba da karatu da su je Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya da ke Kano.

No comments