Manchester United ta samu maki daya da kyar a hannun Chelsea a yau Lahadi a wasan da suka buga tsakaninsu a filin wasa na Stamf...
Manchester United ta samu maki daya da kyar a hannun Chelsea a yau Lahadi a wasan da suka buga tsakaninsu a filin wasa na Stamford Bridge.
Jadon Sancho na Manchester United ne ya zura wa Chelsea kwallo ta farko a minti na 50 a yayin da Jorginho ya ramawa Chelsea a bugun daga kai sai mai tsaron gida a minti na 69.
Wannan sakamakon ya sanya kocin rikon kwarya na Manchester United wato Carrick ya samu maki na farko a gasar Firimiyar ta Ingila bayan nasarar da ya samu a kofin zakarun Turai a tsakiyar makon da ya gabata.
No comments