Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Jihar Bauchi Ya Taya Sabon Shugaban Matasan Jam’iyyar PDP Kadede Murna

  Gwamnan jihar Bauchi, mai girma Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya karbi bakuncin sabon shugaban matasa na jam'iyyar PDP Muhammad Kade...

 


Gwamnan jihar Bauchi, mai girma Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya karbi bakuncin sabon shugaban matasa na jam'iyyar PDP Muhammad Kadede Suleiman  a daren yau a masaukin gwamnatin jihar Bauchi dake Abuja.

Kadade mai shekaru 25 ya ziyarci Gwamnan  ne domin gode ma Gwamna Bala bisa ga irin gudunmawar da ya bayar wajen tsayawar sa  takara wanda ya kai shi da samun nasarar lashe zaben .

Gwamnan ya nuna jin dadinsa bisa yanda matashin ya gwada sa'ar sa kuma yayi nasara Gwamnan yayi kira ga Dukkanin matasa kan su tashi tsaye wajen ganin anyi komai da su a siyasan ce.

Gwamnan yace matasa na da Gagarumin rawar da za su taka kuma lokacin su ne su shigo ayi komai da su Kasar tana bukatar gudumawar su.

Gwamnan yace matashi Muhammad kadade yayi amfani da shawarin su kuma yayi nasara wannan abu ne dake karfafa gwiwa matika. 

Daga Lawal Muazu Bauchi

Mai tallafawa Gwamnan jihar Bauchi kan Sabbin kafofin yada labarai na zamani.

No comments