Gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom, a ranar Litinin ya soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Gwamna Ortom ya ce gwamnatin mulkin soja m...
Gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom, a ranar Litinin ya soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Gwamna Ortom ya ce gwamnatin mulkin soja mafi muni da aka taɓa yi a ƙasar nan ta fi gwamnatin APC mai mulkin ƙasar yanzu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya faÉ—i hakan ne a wani taron manema labarai jim kaÉ—an bayan komawarsa Binuwai É—in daga taron jam'iyyar PDP da aka yi a Abuja.
Ya ce sakamakon taron jam'iyyar tasa ya nuna ƙarara cewa PDP ta shirya don karɓar mulkin ƙasar nan a 2023, yana mai zargin cewa wannan gwamnatin ta gaza a duk al'amuranta.
"Sun yi nasara wajen lalata tattalin arzikinmu da tsaronmu da harkokin rayuwarmu da ma duk wani abu da ya shafi ƙsar nan.
"Na karanta tarihin Najeriya da na waɗanda suka lalata mu ciki har da mulkin soji. Yawanci mukan ce gwamnatin farar hula mafi taɓarɓarewa ta fi gwamnatin mulkin soji.
"Amma a gaskiya gwamnatin mulkin soji mafi lalacewa ta fi gwamnatin APC da ke mulki a yanzu," in ji Gwamna Ortom.
No comments