Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Gwamnatin Neja Ta Bayyana Wuraren Da Boko Haram Ke Iko Da Su A Jihar

Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Matane ya bayyana cewa, ’yan ta’addar Boko Haram sun Æ™wace garuruwa biyar a qananan hukumo...


Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Matane ya bayyana cewa, ’yan ta’addar Boko Haram sun Æ™wace garuruwa biyar a qananan hukumomin Rafi da Shiroto a jihar Neja.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a Minna, babban birnin jihar a ranar Litinin.

Ya yi bayanin cewa, mayaƙan na Boko Haram suna da cikakken iko a Hanawanka, Madaka, a ƙaramar hukumar Rafi da Kurebe, Gussau, Farina Kuka a ƙaramar hukumar Shiroro, wanda hakan ya tilasta wa mazauna karkara yin hijira zuwa wasu wurare.

Ya ce, ’yan ta’addan na tafiya cikin walwala a yankunan da abin ya shafa, suna riÆ™e da nagartattun makamai da kuma muggan makamai.

Matane ya ce, tuni jihar ta sanar da hukumomin tsaro domin É—aukar matakan tsaro na gaggawa.

Ya qara da cewa, “mun kashe sama da Naira biliyan 2 kan jami’an tsaro wajen yaÆ™i da ’yan bindiga da garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka a cikin shekaru biyu da suka wuce. Za mu ci gaba da ba da fifiko ga jin daÉ—in jami’an tsaron da aka tura domin ba su damar kawar da duk waÉ—anda ke da hannu a cikin haramtattun ayyuka tada zaune tsaye.”

“Haka zalika, mun yi kira ga mazauna yankin da su ba da gudummawar ingantattun bayanai game da duk wani motsin da ba su gamsu da shi ba zuwa ga ofisoshin tsaro mafi kusa don É—aukar matakan tsaro. Mun kuma tuntuÉ“i shugabannin gargajiya da na addini da kuma masu ruwa da tsaki don jawo hankalin jama’a don tallafa wa Æ™oÆ™arin gwamnati a ci gaba da yaÆ™i da masu aikata laifuka,” inji shi.

Matane, ya kuma yaba tare da yabawa ƙoƙarin gwamnatin jihar Neja na shawo kan matsalar.

Ya ce, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta kawo ƙarshen ƙalubalen tsaro da ke addabar Jihar.

-Manhaja Blueprint

No comments