Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Ta Ce Kamfanin Twitter Ya Amince Da Sharidodin Da Aka Gindaya Masa

Gwamnatin Tarayya ta ce kamfanin Twitter ya amince da daukacin sharidodin da aka gindaya masa kafin bashi sabon umurnin komawa a...


Gwamnatin Tarayya ta ce kamfanin Twitter ya amince da daukacin sharidodin da aka gindaya masa kafin bashi sabon umurnin komawa aiki a cikin kasar.

Ministan kasa a ma’aikatar kwadago Festus Keyamo wanda ke cikin ‘yan kwamitin da gwamnati ta kafa domin tattaunawa da kamfanin yace sun samu gagarumar ci gaba a ganawar da suke yi.

Keyamo ya ce matakin da shugaban kasa ya dauka akan kamfanin an dauke shi ne domin inganta danganta tsakanin bangarorin biyu amma ba domin korarsa daga Nijeriya ba.

Daga cikin sharidodin da gwamnatin Nijeriya ta gindayawa kamfanin Twitter akwai bude ofishin sa a cikin kasar wanda zai baiwa ‘yan Nijeriya damar kai korafin su da kuma biyan haraji ga gwamnati.

Kamfanin twitter ya harzuka ‘Yan Nijeriya lokacin da ya sanar da aniyarsa ta bude ofishinsa a Ghana maimakon Nijeriya, kasar dake dauke da miliyoyin jama’ar dake amfani da shi fiye da kowacce kasa a nahiyar Afirka.

No comments