Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Zamfara Ta Rantsar Da Kwamishinoni, Masu Bayar Da Shawara Da Manyan Sakatarori

Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin, Honorabul (Dr) Bello Muhammad Matawallen Maradun, ta rantsar da karin kwamishinoni...Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin, Honorabul (Dr) Bello Muhammad Matawallen Maradun, ta rantsar da karin kwamishinoni biyu, masu bai wa gwamna shawara goma, manyan Sakatarori takwas tare da babban mai bincike na jihar Zamfara. 

Haka zalika kafin rantsar da su kamar yadda kundin tsarin Nijeriya ya tanada, sai da aka rantsar da su da Alkur'ani akan cewa ba su da hannu akan matsalar tsaron da ke addabar Zamfara, ko taimakawa masu yin aika-aikar kamar yadda Abdulmalik Saidu Mai Biredi, mai tallafawa gwamnan kan harkokin kafafen watsa labarai na zamani ya labarto. 

Da yake jawabi a wajen rantsuwar Gwamnan jihar Zamfara, ya yi Kira ga sabbin wadanda aka rantsar din, da su yi aiki tukuru wajen tallafawa cigaban sha'anin taro tare da tallafawa cigaban al'ummar jihar Zamfara a wadannan sabbin mukamai da aka rantsar da su akai.

Bikin rantsuwar wanda wakilin mai shari'a Kulu Aliyu ya jagoranta ya samu halartar: Kakakin Majalisar dokokin jihar Zamfara, Honorabul Nasiru Mu'azu Magarya, tsohon mataimakin gwamna, Malam Ibrahim Wakkala Muhammad Liman, Shugaban ma'aikata a fadar Gwamnati Ibrahim Sulaiman Gusau, Tsohon Sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Farfesa. Abdullahi Shinkafi, babban mai bai wa gwamna shawara akan Siyasa da Jam'iyyu Honorabul Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, Sarakuna, Kantomomi, Kwamishinoni, masu bai wa gwamna shawara da manyan daraktoci, shuwagabannin jami'an tsaron Zamfara, Malaman addinin musulunci, masu bai wa gwamna shawara, manyan daraktoci da sauran muhimman jama'a.

No comments