Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnoni Za Su Goyi Bayan Cire Tallafin Man Fetur, Cewar El-Rufai

  Daga Ammar M. Rajab Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya ce idan har ba a cire tallafin man fetur ba, jihohi 35 cikin 36 da yiwuwa...


 Daga Ammar M. Rajab

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya ce idan har ba a cire tallafin man fetur ba, jihohi 35 cikin 36 da yiwuwar ba za su iya biyan albashi ba a shekarar 2022.  Inda ya ce a shirye suke su gwamnoni su goyi bayan cire tallafin man fetur din. 

El-Rufa'i ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja a wajen taron Bankin Duniya kan ci gaban Nijeriya na watan Nuwamban 2021, inda ya jaddada cewa domin a kaucewa hakan gwamnoni a shirye suke su goyi bayan cire tallafin man fetur din kamar yadda majiyarmu ta Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ta labarto. 

El-Rufai ya ce an daidaita kananzir ma da ya fi damun talakawa ma ba tare da an samu matsala ba, a yayin da man dizal ya fi muhimmanci ga masu zirga-zirga shi ma an dade da kayyade shi.

"Wannan tirka-tirka da ake yi game da man fetur abu ne da ya zama wajibi a matsayinmu na kasa mu tattauna kuma mu amince cewa sai an kawo karshensa”.

"Ba za mu iya ci gaba da samar da man fetur ga kasashen dake makwabtaka damu ba, wanda shi ne abin da muke yi. Wa ke amfana da hakan? Don wa muke yi? Wane ne wanda yake amfana? Wanne dan goshin ne ke cin gajiyar wannan kuma me zai sa su rike kasar nan domin biyan bukatar kansu da kuma durkusar da tattalin arzikin Nijeriya?" Ya tambaya.

A cewar El-Rufa'i; "A yanzu haka muna asarar Naira biliyan 250 duk wata kuma dole a kawo karshen wannan. Gwamnatocin Jihohi sun dukufa wajen marawa Gwamnatin Tarayya baya akan haka.

"Muna yin bakin kokarinmu, muna hada kai da masu ruwa da tsaki tare da dora gamsassun hujjoji bisa teburi domin kowa ya fahimci hadarin da kasar nan ke ciki idan aka ci gaba da bayar da tallafin, da kuma alfanun da za a samu (idan aka cire).

"Ba wai kawai kasafin kudin jihohin da karfinsu na gudanar da ayyukan jin dadin jama’a ba, har ma da abin da zai shiga aljihun talakawan Nijeriya kai tsaye wanda zai dauki nauyin duk wani janye tallafi", inji shi.

Ya ci gaba da cewa; “Wannan shi ne matsayar gwamnatocin jihohi kuma mun hadu ne kwanaki kadan da suka wuce domin daukar wannan matsaya.”

El-Rufai ya ce gwamnonin sun ga hatsarin da ke tattare da ci gaba da biyan tallafin man fetur da kuma matakan tallafawa manufofin da ake bukata domin inganta yanayin kasafin kudi, da daidaiton farashi.

Wannan, a cewar shi, za a cimma manufarnan ne ta hanyar tabbatar da cewa an daidaita farashin musaya da kuma kyakkyawan aiki tsakanin manufofin kasafin kudi da na kashe kudin. 

No comments