Rahotanni sun bayyana cewa har yanzu ba a san adadin mutanen da ke hannun ƴan bindiga ba tun bayan harin da aka kai kan hanyar...
Rahotanni sun bayyana cewa har yanzu ba a san adadin mutanen da ke hannun ƴan bindiga ba tun bayan harin da aka kai kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ba a ranar Lahadi.
A jiya Litinin ne gwamnatin Kaduna
da rundunar ƴan sandan jihar ta ce ta ceto mutum 11 bayan musayar wuta da ƴan
sanda da sojoji suka yi da ƴan bindiga.
Sai dai hukumomin har yanzu ba su tantance
yawan mutanen da aka sace ba. Sai dai Jami’an sun ce sun samu motocin matafiya
da dama ba kowa a cikinsu, wasu a cikin daji wasu kuma a gefen hanya.
Harin na hanyar Kaduna zuwa Abuja ya
yi ajalin tsohon ɗan takarar gwamnan Zamfara Alhaji Sagir Hamidu.
Karanta wannan; 'Yan Bindiga Sun Kashe Tsohon Dan Takarar Gwamna a Zamfara A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna
Karanta wannan; An Yi Jana'izar Dan Siyasar Zamfara Da 'Yan Bindiga Suka Kashe A Hanyar Abuja
No comments