Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Harin Da 'Yan Bindiga Suka Kai Gidan Yari A Jos Ya Zo Mana Da Mamaki -Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta ce ta yi mamakin yadda aka kutsa aka kai wa gidan yarin na Jos hari. Gwamnatin jihar Filato ta ce hari...


Gwamnatin jihar Filato ta ce ta yi mamakin yadda aka kutsa aka kai wa gidan yarin na Jos hari.

Gwamnatin jihar Filato ta ce harin na ranar Lahadi ya zo mata da ba-zata kasancewar gidan yarin na tsakiyar wurare masu tsaron gaske da suka hada da ofishin 'yan sanda da na jami'an tsaron farin kaya wato DSS da kuma wata babbar kotu.

"Abin takaici ne yadda har 'yan bindiga suka iya kutsawa wannan wuri mai tsaro kuma suka so su yi barna idan ban da Allah ya kiyaye", in ji kwamishinan yada labaran jihar, Dan Manjang.

Sai dai kwamishinan bai yi bayani ba kan ko an samu rashin rai da sakin daurarru, inda ya ce "muna tattara bayanai kuma za mu sanar da ku saboda ba ma son yada labarin kanzon kurege."

Ita ma hukumar gidan yarin ta Nijeriya, a wata sanarwa, ta tabbatar da faruwar al'amarin, sai dai ta ce jami'an tsaro sun yi galaba a kan maharan.

Francis Enahoro, a sanarwar ya ce "'Yan bindigar dai sun bayyana ne da misalin karfe 5:20 na yammar ranar Lahadi inda kuma suka yi musayar wuta da ma'aikatan gidan yarin. To sai dai sun samu sun kutsa cikin gidan mazan bayan da suka yi galaba kan jami'an namu."

To sai dai Enahoro ya kara da cewa "bayan la'akari da cewa sun fi mutanenmu karfin makamai sai muka nemi dauki daga sauran abokan aikinmu jami'an tsaro kuma nan da nan aka kawo mana dauki inda aka rutsa maharan a cikin gidan yarin."

Sanarwar ta kara da cewa yanzu komai ya lafa kuma jama'a su kwantar da hankalinsu.

To sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayani ba dangane da ko maharan sun samu nasarar sakin wasu fursunoni da kuma yadda aka yi da su bayan da aka rutsa su a gidan yarin.

Har kawo yanzu dai babu wani da ya fito ya yi ikrarin kai wannan hari. Sannan hukumar gidan kaso ta Nijeriya da ma gwamnatin jihar Filato ba su bayyana mutanen da suke zargi da kai wannan hari ba.

Kungiyar Boko Haram dai na ci gaba da kai hare-hare a yankin arewa maso gabashi, inda a baya-bayan nan suka yi ajalin wani babban soja mai mukamin Janar.

Har wa yau, akwai 'yan bindiga da ke garkuwa da mutane a yankin Arewa maso yamma da ta tsakiya wadanda su ma zargin ka iya fada wa kansu.

(BBC)

No comments