Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Honorabul Babawo Na Kowa Da Kowa Ne, Inji NASS

Daga Fatima Idris, Zariya A cikin makon nan ne Dan majalisa tarayya mai wakiltar karamar Sabon Gari ta jihar Kaduna wato Honorab...


Daga Fatima Idris, Zariya

A cikin makon nan ne Dan majalisa tarayya mai wakiltar karamar Sabon Gari ta jihar Kaduna wato Honorabul Garba Datti Muhammad Babawo ya shiryawa jama'ar mazabunsa hanyar dogaro da kai tare da ba su tallafi kudi domin fara abin da suka koya.

Daga cikin abubuwan da aka koyawa daruruwan jama'ar sun hada da koyan kiyon dabbobi akwai bangaren koyan wanke gashi da koyan dinki da dai sauransu.

Jama'ar da suka sami wannan garabasar sun fido daga gundumomin da ke karamar Hukumar ta Sabon Garin kamar Samaru  da Jama'a da Cikaji da dai sauransu .

Taron an gudanar da shi ne a wurare daban-daban ciki harda dakin taro na TJ dake GRA Zariya.

Haka zilika taron an kwashe kwanaki Uku cur ana horar da jama'a ilmi a bangarori daban-daban.

Malamai ne daga cibiyoyin ilmi suka gabatar da mukaloli a bangarori da dama bisa kulawar hukumar CMD ta kasa.

Nasiru Umar Abdullahi da aka fi sani da NASS matashi ne a cikin matasa masu taimakawa shi Honorabul Garba Datti Muhammad Babawo a bangarori daban-daban a karamar hukumar Sabon Gari.

Nasiru Umar Abdullahi (NASS) ya bayyanawa wakiliyarmu manufofin tafiyar Honorabul Garba Datti Muhammad Babawo daga karamar hukumar har zuwa tarayya jim kadan bayan sun damka wa jama'ar da aka horar takardar shaida a wajen taron. 

Da farko NASS ya fara ne da godiya ga Allah bisa ga yadda ya ga an fara taron lafiya an kammala lafiya.

Bayan haka kuma ya ce, wannan kokarin da shi Honorabul Garba Datti Muhammad Babawo ke yi yana nuna wa duniya ne cewa shi na kowa da kowane.

Matashin ya kara da cewa idan jama'ar karamar Hukumar Sabon Gari za su lura duk inda Babawo ya gudanar da lamarin taimako to za ka ga ba mutum daya ke amfana da shi ba sai dai al'umma .

Matashin ya bayar da misali da daruruwan mutanen da aka koyawa sana'ar dogaro da kai wanda fatan shi dan majalisa shi ne wanda aka koya wa su ma su koyawa wasu don ci gaban jama'a baki daya. 

Don haka ne yasa muke mara masa baya kuma ya ce za su ci gaba da mara masa baya. 

Kuma matashin dan siyasar ya yi kira ga matasan karamar hukumar Sabon Gari baki daya cewa su zo a tafi tare da su ka da su bari a bar su a baya domin Babawo alheri ne ga matasa baki daya.

Ya ce dalili ko shi ne Honorabul Garba Datti Babawo ba shi da mugunta illa alheri burinsa shi ne duk abin da ya samo ya kai gida a taru a amfana da shi wanda hakan ne wakilci na gari ba a ci shiru yake ba.

Karshe Nass ya mika godiya da jinjina ga mai gidan nasa bisa kokari da jajircewa irin nasa a bangarorin da yake bayar da gudummawa ga al'ummarsa.

Kuma ya yi yabo ga dukkan masu tallafa mishi wajen gudanar da harkokinsa musamman kamarsu Alhaji Ado Samaru da Alhaji Uwaisu da su Babawo Karami ya ce wadannan mutane gaskiya suna kokarin gaske Allah ya bar zumunci.

Ya kuma yi roko ga dukkan wanda suka sami tallafi don gudanar da sana'a a yanzu da lokutan baya su yi amfani da abin da suka samu ta hanyar da ya dace.

Ya ce hakan ne zai karawa shi Honorabul Garba Dattin kwarin guiwar bada wani tallafin.

Binciken da wakiliyarmu ta yi shi ne da yawa daga cikin wadanda suka samu tallafin dan majalisar  a lokutan baya da kuma yanzu suna amfani da shi ta hanyar da ya dace hakan yasa farin jininsa ke karu wa a halin yanzu.

Haka zalika bincike ya tabbatar da cewa kokarin da Dan majalisan ke yi a fadin karamar hukumar da jihar har zuwa tarayya na karawa jam'iyyarsa ta APC farin jini. 

Yanzu haka da yawan mutane na yi wa Honorabul Garba Datti Muhammad Babawo fatan alheri har da 'yan Adawa.

No comments