Daga Fatima Idris Zariya A ranar Litinin 22 ga watan Nuwambar shekarar 2021 ne Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar karamar huku...
Daga Fatima Idris Zariya
A ranar Litinin 22 ga watan Nuwambar shekarar 2021 ne Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna Honorabul Garba Datti Muhammad Babawo (Ogan Oga) ya sake Gwangwaje wasu daga cikin al'ummar mazaɓarsa da kyautukar da ta sanya su farin ciki tare da godiya ta musamman
Kyautar kuwa ta haɗa da sabbin na'urorin sanyaya kaya (Deep-freezer) guda Talatin da biyar (35) da Keken ɗinki guda ɗaya.
Wakiliyarmu ta shaida yadda lamarin ya gudanar inda ta labarto cewa; Honorabul Garba Datti Muhammad Babawo ya gabatar da bayar da tallafin ne a bangarori daban-daban.
Baya ga bada na'urar sanyaya kayan abinci guda 35, dan bajalisar ya dauki dauyin jama'arsa maza da mata su 300 domin horar da su sana'ar dogaro da kai tare da bai wa kowa jarin (somin tabi).
Take dan majalisar ya ba su naira Dubu ashirin da biyar ga duk wanda ya sami horon bisa kulawar hukumar CMD ta kasa.
Tuni kuma ya kara komawa sashen kiwon lafiya inda a nan ma ya tufaye alkawarin da ya dauka karo na shida (6) wanda yanzu haka likitoci na can suna gududanar da aiki ga yara da manya kuma jama'a na ta mika godiyarsu.
Bisa haka ne wakiliyarmu ta nemi jin ta bakin dan majalisar akan ko me ya ja hankalisa da ya dukufa wajen gudanar da irin wadancan ayyukan na bayar da tallafi ga jama'arsa?
Honorabul Garba Datti Muhammad Babawo sai ya kada baki ya ce, babban dalilin da ya sa shi gudanar da wadancan ayyukan shi ne, neman yardar Ubangiji ne kawai.
Dan majalisar ya kara da cewa, tarihi ya nuna cewa duk wanda ya taimaki wani to Allah zai taimake shi.
Bayan haka ya kara da cewa, tun farko dama shi maganar taimakawa jama'a wajibi ne akan kowa don haka ya dorawa kanshi wannan aiki.
Ya ce fatansa shi ne Allah ya karbi aikin nasa yasa ya sami ladan gobe kiyama da dukkan wanda suka sa hannu lamarin ya tabbata.
Karshe ya yi godiya ga jama'ar nasa bisa yadda suke bin doka da oda wajen samun tallafin.
Kuma ya yi jinjina ga masu taimaka mashi a bangarori daban-daban ya yi tuni ya yi fatan Allah ya bar su tare kuma ya biya masu bukatarsu baki daya.
Kana ya yi fatan Allah ya karawa shugaban kasa lafiya tare da Gwamnansa na jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-Rufa'i. Dukkansu ya yi fatan Allah ya ci gaba da ba su kyakykyawan jagoranci da samun nasara gami zaman lafiya a kasa baki daya.
Daga cikin wanda suka sami tallafin a bangaren mata akwai shugaban mata a jam'iyyar APC na shiyyar Samaru, Ita ma godiya ta yi tare da jinjina ga Dan majalisar na su Honorabul Babawo bisa yadda yake duba mata a siyasance a fadin karamar hukumar ta Sabon Gari.
A karshe shugabar ta yi fatan alkhairi gare shi tare da yin kira ga sauran 'yan siyasa da su yi koyi da halinsa na alheri.
No comments