Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ibrahimovic Ya Ci Kwallonsa Na 400 A Wasannin Lig-Lig

  Zlatan Ibrahimovic ya ci kwallonsa na 400 a wasannin Lig-Lig bayan kwallon da ya ci a wasan da AC Milan ta yi nasara a kan Roma da ci 2 -1...

 


Zlatan Ibrahimovic ya ci kwallonsa na 400 a wasannin Lig-Lig bayan kwallon da ya ci a wasan da AC Milan ta yi nasara a kan Roma da ci 2 -1 a gasar Seria A, kuma na 150 a gasar ta Italiya.

Nasarar da Milan ta samu ya sa ta zama ta hada maki 31-31 dai dai da Napoli da ke jagorantar teburin gasar.

Ibrahimovic, mai shekaru 40, ya fara cin kwallo ne a mintuna na 25 da soma wasa kafin Franck Kessie ya na biyu a bugun Finareti.

Milan ta Karkare wasanta da ‘yan wasa goma bayan da aka bai wa Theo Hernandez jan kati, inda Stephan El Shaarawy ya zura kwallo a ragar tsohuwar kungiyarsa.

Itama Napoli ta samu nasara a kan Salernitana da ci 1-0, kuma kamar Milan, sun ci wasanninsu 10 cikin 11 da suka fafata a wannan kakar.

No comments