Tsohon shugaban Nijeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana goyan bayansa ga jagorancin shugaban rundunar sojin kasa La...
Tsohon shugaban Nijeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana goyan bayansa ga jagorancin shugaban rundunar sojin kasa Laftanar Janar Faruk Yahaya na shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi kasar kamar yadda RFI ta labarto.
Babangida ya ce duk da yake Nijeriya na fuskantar matsalolin tsaro a wasu sassan kasar, rundunar sojin ta bada gagarumar gudumawa wajen tunkarar su tunda aka nada sabon babban hafsan sojin.
Shima a na shi bangare, tsohon shugaban kasa Janar Abdusalami Abubakar ya bayyana gamsuwa da irin rawar da shugaban sojin ke takawa wajen magance matsalolin tsaron da suka mamaye sassan Nijeriya.
Abdussalam ya yabawa matakan da Janar Yahaya ke dauka na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a bangaren tsaro domin samun goyan baya da hadin kan da ake bukata wajen samun nasarar yakin da suke yi na kakkabe ‘Yan ta’adda da masu aikata laifuffuka a cikin Nijeriya.
Tsohon shugaban ya ce ziyarar cibiyoyin sojin da babban Hafsan ke yi domin ganawa da dakarun kasar na da matukar tasiri wajen jin ta bakin sojojin da kuma shawo kan matsalolin da suke fuskanta.
Laftanar Janar Yahaya ya ce ya ziyarci Jihar Neja ne domin ganawa da sojojin dake rundunar TRADOC da zummar inganta horan da suke bayarwa da kuma dabarun yaki.
Shugaban sojin ya ce ziyarar tsoffin shugabannin ta ba shi damar tattaunawa da su akan halin da ake ciki dangane da irin matakan da yake dauka.
Janar Yahaya yace samun goyan baya daga masu ruwa da tsaki akan harkar tsaro da kuma ‘yan kasa zai taimakawa sojojin wajen magance matsalolin tsaron suka addabi kasar.
No comments